Kungiyoyin Arewa 75 sun sa miliyan 100 ga duk wanda ya iya kamo Shugaban IPOB, Kanu
- Northern Consensus Movement ta na shelar a cafko mata Nnamdi Kanu
- Duk wanda ya kawo Nnamdi Kanu cikin koshin lafiya, zai samu N100m
- Kungiyoyin Arewan suna so a cigaba da shari’a da shugaban IPOB a kotu
Gamayyar kungiyoyin Arewa a karkashin Northern Consensus Movement sun bada sanarwar kyautar kudi ga wanda zai iya cafko mata Mazi Nnamdi Kanu.
A ranar Alhamis, kungiyar Northern Consensus Movement ta ce za ta bada Naira miliyan 100 a matsayin tukuici ga duk wanda ya kawo shugaban kungiyar IPOB.
Jaridar The Nation take cewa wadannan kungiyoyi na Arewa su na so a dawo da Nnamdi Kanu gida ne domin ya cigaba da fuskantar shari’ar da ake yi da shi.
KU KARANTA: Matasan Arewa sun yi magana a kan yunkurin kashe Shugaban EFCC
Kungiyoyin sun bayyana haka da suke zanta wa da ‘yan jarida a Abuja, su ka zargi Kanu da dakarun ESN da kitsa harin da aka kai wa ‘Yan Arewa a Kudu.
Dr. Awwal Aliyu ya yi magana a madadin Northern Consensus Movement, ya na rokon Amurka, Ingila da kasashen Turai su izo keyar Kanu, ayi masa hukunci.
Vanguard ta rahoto Dr. Awwal Aliyu ya na jawabi:
“Kungiyar Northern Consensus Movement, gamayyar kungiyoyin Arewa masu zaman kansu fiye da 75 sun daukarwa kansu, a matsayinsu na ‘yan kasa cewa:
KU KARANTA: Kotu ta bada belin Mai shekara 52 da ‘danta, da ake zargi da laifi
Laifuffukan Shugaban IPOB, Nnmadi Kanu
“Ana neman Nnamdi Kanu da laifin laifuffuka, da haddasa kashe-kashen da aka yi wa mutanen Arewa a yankin Kudu maso gabas ta hanyar kalaman kiyayyarsa.”
“Muna so ya amsa laifuffukansa na kisan rayuka da barnata dukiyar mutanen Arewa da su ke zaune a Kudu maso yammacin Najeriya, suna kasuwancinsu na halal.”
“Saboda haka mun sa kyautar kudi na N100m a matsayin rabon wanda zai iya kawo mana da shi da ransa, cikin koshin lafiya, ba tare da an yi masa rauni ba.” inji Aliyu.
Kungiyar ta na so a kawo mata wannan mutum, ta kai shi wurin jami’an tsaro, su cigaba da shari’a da shi, ya amsa laifuffukansa na cin amanar kasa da ta’addanci.
A jiya ne aka ji cewa wasu 'yan bindiga sun sace dalibai a jihar Kebbi. Wadannan miyagu sun yi amfani da motar mahaifin wata daliba wajen sace daliban makarantar.
Daga baya wani 'Dan majalisar wakilai a majalisar tarayya ya gaskata faruwar wannan lamari.
Asali: Legit.ng