EFCC ta cafke wasu mutum 3 da ake zargi da yin kudin jabu

EFCC ta cafke wasu mutum 3 da ake zargi da yin kudin jabu

  • Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta cafke wasu mutum uku da zargi da buga kudaden bogi
  • Mutum ukun da 'yan sanda suka damke kuma suka mikawa EFCC suna harkallarsu a kasashen duniya ba Najeriya kadai ba
  • An gane cewa sun buga kudaden da suka hada da dalar Amurka, Fam da Euro kuma suna aikin a kasashen duniya

Ofishin hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa (EFCC) ta fara bincike kan zargin wasu mutum uku da ake da hada kai wurin cuta tare da buga kudin jabu.

Wadanda ake zargin sun hada da Sylvanus Ireka Ifechukwu, Patrick Chima ibiam da Ajimijere Mathias Adegbenro, Channels TV ta ruwaito.

'Yan sanda na bangaren bincike na musamman dake hedkwatar hukumar ta Obalende, jihar Legas sun yi kamen a ranar 30 ga watan Afirilun 2021 kuma suka mika su gaban EFCC domin cigaba da bincike.

KU KARANTA: Da duminsa: EFCC ta gurfanar da jami'an gwamnatin Sokoto 5 kan damfarar N500m

EFCC ta cafke wasu mutum 3 da ake zargi da yin kudin jabu
EFCC ta cafke wasu mutum 3 da ake zargi da yin kudin jabu. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kurmushe gidan dan majalisa a Imo, sun sheke maigadi

Ba a kasar Najerya kadai suke harkallarsu ba

Wadanda ake zargin da buga kudaden jabu an gano cewa suna da hadaka da abokan aiki a fadin duniya, Channels TV ta wallafa.

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin suna harkallarsu ne a kasar Brazil kuma ana zargin suna buga kudaden kasashen ketare masu daraja da suka hada da dalar Amurka, Fam da Euro.

Inda suke samu masu siyan kudaden bogin

An gano cewa suna samun masu siya ne a wurare da suka hada da otal, ofishin 'yan canji da kuma wuraren shakawata a birnin Legas.

Bayan kama su, an samu wasu abubuwan aikinsu a wurinsu. Kamar yadda hukumomi suka tabbatar, wadanda ake zargin za a mika su gaban kotu nan babu dadewa.

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 'yan kasar Chaina a jihar Taraba.

Lamarin ya faru a daren Litinin a wani wurin hakar ma'adanai a yankin Arufu dake karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba.

David Misal, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Channels TV a wata hira ta wayar salula a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel