Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon Manajan fitaccen banki shekaru 12 a gidan yari

Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon Manajan fitaccen banki shekaru 12 a gidan yari

  • Wata kotun Ikeja ta yankewa tsohon manajan daraktan tsohon Bank PHB, Francis Atuche, shekaru 6 a gidan yari kan satar N25.7 biliyan
  • Kotun ta sake yankewa tsohon CFO, Ugo Anyanwu hukuncin shekaru shida a gidan gyaran hali duk a kan laifin
  • Mai shari'a Lateefat Okunnu wacce ta shugabanci kotun ta ce EFCC ta tabbatar mata da cewa sun saci kudin ne ba bashi suka karba ba kamar yadda suke ikirari

Ikeja, Legas

Francis Atuche, tsohon manajan daraktan tsohon bankin PHB Plc, ya samu hukuncin shekaru shida a gidan yari kan damfarar makuden kudade har N25.7 biliyan.

Mai shari'a Lateefat Okunnu ta babbar kotun dake Ikeja a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni ta hada da tsohon jami'in kudi na bankin, Ugo Anyanwu shekaru shida a kan laifin, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci

Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon MD fitaccen banki shekaru 12 a gida yari
Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon MD fitaccen banki shekaru 12 a gida yari. Hoto daga Tekumbo AremoOdua
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnan Neja yayi fallasa, ya bayyana yadda 'yan bindiga ke hada kai da jami'an gwamnati

Legit.ng ta tattaro cewa alkalin ta sallama tare da wanke matar Atuche mai suna Elizabeth. A yayin yankewa su biyun hukunci, mai shari'ar ta ce EFCC ta tabbatar da kokenta kuma babu shakka hakan ya faru sama da shekaru 10 da suka gabata.

Sace N25.7b aka yi ba bashi ba

Tsohon shugaban bankin, matarsa da Anyawu aka zarga da sacewa tare da hada kai wurin watanda da N25.7 biliyan na bankin.

An gurfanar dasu a 2011 a gaban Okunnu amma basu amsa laifin da ake zarginsu da shi ba.

Amma kuma yayin karanto hukuncin, alkalin ta tabbatar da koken EFCC na cewa sace kudin aka yi ba bashi aka karba ba kamar yadda Atuche yace, The Cable ta ruwaito.

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da ma'aikatan hukumar fansho ta makarantar firamare a kan zarginsu da ake da waskar da kudi har N553.985,644.1.

Kudin an adana shi ne domin biyan malaman makaranta da suka yi ritaya kudin sallama da na fansho, Daily Trust ta ruwaito.

Ma'aikatan sun hada da: Abubakar Aliyu, Hassana Moyi, Haliru Ahmad, Kabiru Ahmad da Dahiru Muhammad Isa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng