Duba dankareriyar mota kirar Roll Royce Cullinan Suv ta N100m da tsohon sanata ya siya

Duba dankareriyar mota kirar Roll Royce Cullinan Suv ta N100m da tsohon sanata ya siya

  • Sanata Dino Melaye a halin yanzu baya majalisar dattawa amma har yau yana haskaka kafafane sada zumunta
  • Tsohon sanatan mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma ya wallafa hoton sabuwar motarsa kirar Rolls-Royce Cullinan SUV
  • Hotunan tsuleliyar motar ya janyo dubban tsokaci game da yanayin rayuwa mai tsada ta tsohon dan siyasan

Sanata Dino Melaye, tsohon dan majalisa da ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa ta takwas, ya wallafa daya daga cikin motocin alfarmar da ya mallaka a garejinsa kirar Rolls-Royce Cullinan SUV.

Melaye, jigo a jam'iyyar PDP ya yi nasarar lashe zaben kujerar sanatan yankinsa a 2019 amma kotun kararrakin zabe ta fattakesa kuma ta bukaci a yi sabon zabe bayan abokin hamayyarsa, Sanata Smart Adeyemi ya kai kara.

KU KARANTA: Buhari zai ziyarci Borno, zai kaddamar da gidaje 4,000 na 'yan gudun hijira, Zulum

Duba dankareriyar mota kirar Roll Royce Cullinan Suv ta N100m da tsohon sanata ya siya
Duba dankareriyar mota kirar Roll Royce Cullinan Suv ta N100m da tsohon sanata ya siya. Hoto daga Dino Melaye
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci

Sanata Adeyemi daga bisani ya lashe zabe inda ya baje Melaye. Tun bayan kayen da ya sha, yanayin rayuwar waddakar sanatan tana ta karade kafafen sada zumunta inda yake wallafa hotunan zagaye kasashen duniya da yake.

Sanata Melaye bai manta da mabiyansa na Facebook ba tunda ya gangara can ya wallafa hotun dankareriyar motarsa.

Darajar motar

Wani shafi wanda ya kware a bayyana kudaden motco ya bayyana kudin motar da naira miliyan dari da goma sha bakwai da dubu dari tara da casa'in.

Tsokacin jama'a:

Babu shakka ko da gani an san jama'a ba zasu yi kasa a guiwa ba wurin yin tsokaci kala-kala. Hakan ce kuwa ta kasance.

Daya daga cikin tsokacin da ya baiwa jama'a mamaki shine na wani mai amfani da Instagram mai suna Unique motors.

Tsokacin ya ce: "Yallabai, akwai sauran kudin da zaka cikawa unique motors. Dukkan kokarin samunka da Moses ya faskara."

A wani labari na daban, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya zargi wasu 'yan siyasa da jami'an gwamnati da zama masu baiwa 'yan bindiga bayanai.

Leadership ta ruwaito cewa gwamnan yayi wannan zargin ne a ranar Talata, 15 ga watan Yuni yayin kaddamar da hukumar 'yan sintirin ta musamman.

Bello yayi ikirarin cewa wasu jami'ai yanzu su ke kaiwa 'yan bindiga bayanan siriri domin samun kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng