Minista ta yi awon gaba da Dala miliyan 37 - Shugaban EFCC ya fadi dabarar barayin gwamnati
- Abdulrasheed Bawa ya koka game da yadda ake satar dukiyar al’umma
- Shugaban EFCC yace akwai wata Minista da ta yi sama da fadi da $37m
- Bawa ya ke cewa ana wawurar kudi ta hanyar mallakar gidaje a Najeriya
Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, Abdulrasheed Bawa, ya ce ana tafka sata a bangaren gidaje.
Jaridar Punch ce ta rahoto Mista Abdulrasheed Bawa, ya na wannan bayani a ranar Larabar nan.
Da ya bayyana a gidan talabijin na Channels TV, sabon shugaban hukumar ta EFCC ya ce kusan 90% na satar da ake yi, suna bi ne ta hanyar mallakar gidaje.
KU KARANTA: Mun nemi mu biciki bidiyoyin Gandollar, amma abin ya gagara - Hukuma
Bawa ya bayyana yadda suka gano wata Minista da ta saye wani gida na Dala miliyan $37.5 a hannun wani banki, kuma nan take ta fara biyan Dala miliyan 20.
Shugaban hukumar ya bayyana wannan ne da yake magana a shirin Sunrise Daily da aka yi jiya.
A jawabinsa, Bawa bai iya kama sunan wannan Minista ba, sannan bai fadi bankin da ya saida wa mata gidan nan ba, abin da kurum ya bayyana shi ne mace ce.
“Daga cikin matsalolin da ake samu a kasar nan shi ne ta harkar saida gidaje. Kashi 90 zuwa 100 na kudin da ake sace wa, duk ta nan ne.” inji Abdulrasheed Bawa.
KU KARANTA: Ba za mu ba ku kunya ba, za mu doke APC a 2023 – PDP ga ‘Yan Najeriya
“Mun binciki wani lamari wanda wani manajan banki ya yanki wani gida ya ba wata Minista, aka yarda za a saya a kan $37.5, bankin ya tura mota ta dauko kudi.”
Hada-kai da bankuna
A cewar Bawa, nan take wannan Minista ta bada $20m daga cikin kudin gidan. “Ba don bankin ba, da Ministar ba za ta iya shan fadi da $20m daga hannun wani ba.”
Bankin ya yi nasarar karbar wannan kudi, daga baya wani Lauya ya dauko takardun, ya yi ikirarin shi ya saye gidan. Bawa bai fadi ko Ministar tana ofis har yau ba.
A jiya kun ji cewa shugaban EFCC ya ce yaki da cin hanci da marasa gaskiya a Najeriya yana neman ya fi karfinsa, sai dai Abdulrasheed Bawa ya ce yana bakin kokari.
Bawa ya ce an sha yi masa barazanar kashe shi, Bawa ya ce wasu manyan barayin kasar ne su ka taso shi a gaba, ya kuma ce cin hanci ya yi katutu wajen bada kwangiloli.
Asali: Legit.ng