Girma ya fadi: An kama Uwa da ‘Danta da sa'o'insa 2 da laifin sata, an kai su gaban Alkali

Girma ya fadi: An kama Uwa da ‘Danta da sa'o'insa 2 da laifin sata, an kai su gaban Alkali

  • Wata mata mai shekara 52 ta bayyana a kotu bisa laifin satar babur a Osun
  • Ana zargin wannan Baiwar Allah da ‘danta, da wasu mutane da wannan laifi
  • Kotu ta bada belin wadanda ake tuhuma a kan kudi N50, 000 tare da jingina

Jami’an ‘yan sanda sun gurfanar da wata mata da ‘danta bisa zargin laifin satar babur. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun gurfanar da wannan Baiwar Allah tare da ‘danta, da wasu mutum biyu da ake zargi da aikata laifin a Osun.

An shigar da karar wadannan mutane hudu a kotun majistare na Ile-Ife, jihar Osun a ranar Laraba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace Dalibai rututu a Kebbi

Jaridar The Nation ta bada sunayen wadanda ake tuhuma a kotu da Patience Ayube, mai shekaru 52, da ‘danta, Josiah Ayube, ‘dan shekara 23 a Duniya.

Har ila yau akwai Oluwaseun Joseph da Friday Emmanuel masu shekaru 22 da 20 da haihuwa.

Ana zargin wadannan mutane da laifin satar wani babur kirar Honda mai lambar rajista, EKY 533 QM, sun sace babur din ne a hannun wani Emmanuel Akpan.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ‘yan sanda sun yi wa babur din kudi ne a kan N285, 000.

KU KARANTA: Babu shirin soke tsarin NYSC a Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Gwamnan Osun
Gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Lauyan rundunar ‘yan sanda, ASP Abdullahi Emmanuel, ya shaida wa kotu cewa mutanen hudu sun jibgi Emmanuel Akpan, suka yi gaba da abin hannunsa.

Yadda shari'a ta soma kasancewa

‘Yan sanda sun ce babu mamaki wadanda ake tuhuma sun tada hankalin jama’a wajen yin wannan aiki. Da aka je kotu, duk sun ce ba su aikata laifin ba.

Lauyan da ya tsayawa wadanda ake zargi, Olalekan Babatunde, ya nemi kotu ta bada belinsu. Alkali A.I Oyebadejoya amince da hakan a kan N50, 000 da jingina.

Dazu kun ji cewa ‘Yanuwa suna tuhumar wani Saurayi da kashe ‘Yar yarinyarsu mai shekara 3 a Katsina, yarinyar da aka kashe kanwa ce a wurin saurayin.

Wannan matashi da ya shiga zargi ya kawo wasika da sunan cewa masu garkuwa da mutane sun aiko takarda, sun bukaci a biya fansa ko su kashe yarinyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel