Hukumar EFCC za ta shigar da sababbin kara 800 domin daure barayi inji Abdulrasheed Bawa

Hukumar EFCC za ta shigar da sababbin kara 800 domin daure barayi inji Abdulrasheed Bawa

  • Abdulrasheed Bawa ya cika kwana 100 da zama Shugaban Hukumar EFCC
  • Bawa ya ce EFCC za ta shigar da kara 800 a kotu tun da an dawo yajin-aiki
  • EFCC za ta sa kafar wando daya da barayin kasa da ‘yan damfaran zamani

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta ce ta shirya shigar da sababbin kara 800 na satar dukiyar kasa a kotu.

Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana wannan a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, 2021, yayin da yake magana a birnin tarayya, Abuja.

Abdulrasheed Bawa ya yi magana da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa kamar yadda duk shugabannin ma’aikatu da hukumomi suka saba duk mako.

KU KARANTA: An gano tsohuwar Ministar da EFCC ta ke nema da laifin satar Biliyoyi

Jaridar Today NG ta rahoto Bawa yana cewa kara 800 za su dumfari kotu da su, mafi yawan shari’ar sun shafi satar kudin al’umma ne da kuma damfara.

A halin yanzu damfara ta kafar yanar gizo wanda aka fi sani da Yahoo-Yahoo ta yi kamari sosai.

Bawa ya fada wa manema labarai cewa yajin-aiki na tsawon watanni biyu da malaman shari’a suka yi ne ya jawo aka gaza shigar da wadannan kara da wuri.

Kwana 100 a ofis

Premium Times ta ce Bawa ya cika kwanaki 100 da shigansa ofis, don haka ya yi bayanin irin nasarorin da ya samu, daga ciki har da daure Francis Atuche.

Abdulrasheed Bawa
Shugaban hukumar EFCC, Malam Abdulrasheed Bawa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Minista ya bada shawarar a sa ido a kan Facebook, Twitter, WhatsApp

Mista Francis Atuche ya taba rike shugaban wani banki a Najeriya. A makon nan aka yanke masa daurin shekaru shida a kurkuku bayan samun sa da laifin satar N26b.

Orji Uzor Kalu

Da yake bayani, shugaban hukumar ta EFCC ya sha alwashin sake shiga kotu da tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, wanda kotu ta wanke kwanaki.

Hukumar EFCC ta yi nasarar daure Orji Uzor Kalu a gidan kurkuku, amma daga baya kotun koli ta fito da shi saboda wasu matsaloli da aka samu a wajen shari’arsa.

Kun ji Bawa a matsayinsa na shugaban hukumar EFCC ya ci alwashin sake gurfanar da Kalu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel