Shugaban EFCC ya fallasa tsohuwar Ministar da ake zargi da laifin satar Naira biliyan 15
- Abdulrasheed Bawa ya ce babu Minista mai-ci da ake zargi da wawurar N15.2bn
- Shugaban hukumar EFCC ya yi karin haske kan wata magana da yayi kwanan nan
- EFCC ta ce ba kowa ake zargi da facaka da 37m ba face Diezani Alison-Madueke
Bayan kwanaki da bankado wani sirri, shugaban hukumar EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ya tona tsohuwar Ministar da suke zargi da satar kudi.
Dazu nan ne Mista Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa Diezani Alison-Madueke ce wanda ake tuhuma da laifin karkatar da fam Dala miliyan 37.5.
Jaridar Tribune ta fitar da rahoto a yau, ta ce Mista Abdulrasheed Bawa ya bayyana wannan a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, 2021, a birnin tarayya.
KU KARANTA: EFCC da AMCON na rikici kan dukiyar da Minista ta sace
Ba a Gwamnatin Buhari aka yi laifin ba
Bawa ya kama sunan Ministan ne yayin da yake karin haske game da wani jawabi da hukumar EFCC ta fitar, ta na cewa tana binciken wata Minista.
Majiyar ta ce shugaban EFCC, ya yi watsi da rade-radin da wasu ke yi na cewa a gwamnatin Muhammadu Buhari aka samu wanda ya yi wannan barna.
Da yake karin haske, Abdulrasheed Bawa bai yi karin bayani a kan halin da ake ciki a binciken tsohuwar Ministar man kasar watau Alison-Madueke ba.
Idan aka yi lissafi a kudin gida na Najeriya, abin da ake tuhumar Diezani Alison-Madueke da karkatarwa daga baitul-mali, ya haura Naira Biliyan 15.
KU KARANTA: An kama wadanda su ka sace kudin fansho a Sokoto - EFCC
Madueke ta rike Ministar man fetur na fiye da shekaru hudu a gwamnatin Goodluck Jonathan, kafin nan Ummaru ‘Yar’adua ne ya nada ta Ministar sufuri.
EFCC ta kama sunan wannan Baiwar Allah ne domin kurum a bada misali, a cewar Mista Bawa.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a karkashin Abdulrasheed Bawa, ta ce a shirye take wajen ganin ta yi maganin barayin kasa.
Idan ba ku manta ba, a baya, Bawa ya ce ne wata Minista ta hada-kai da banki sun sha kwana da wasu makudan kudi ta hanyar sayen wani katafaren gida.
Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa ya ce barayin gwamnati su ka kan wawuri kudi ta hanyar mallakar gidaje.
Asali: Legit.ng