Buhari ya tuna da mutanen da aka kashe ‘yanuwansu a rikicin zaben 2011, ya ba su aiki

Buhari ya tuna da mutanen da aka kashe ‘yanuwansu a rikicin zaben 2011, ya ba su aiki

  • A shekarar 2011 wasu fusatattu suka hallaka masu aikin bautar kasa na NSYC a jihar Bauchi
  • Gwamnatin Tarayya ta ce ta ba ‘yanuwan wadannan Bayin Allah da aka yi wa kisan gilla aiki
  • Muhammadu Buhari ya dauki wannan mataki domin a ragewa wadanda abin ya shafa radadi

This Day ta ce Muhammadu Buhari ya amince a ba mutane 10 aiki a gwamnati. Wadannan mutane sun rasa ‘yanuwansu shekaru goma da suka wuce a rikici.

A sakamakon rikicin da ya barke bayan zaben 2011, wasu masu bautar kasa sun rasa ransu, don haka gwamnatin tarayya ta yanke shawarar ba ‘yanuwansu aiki.

Mai girma Ministan wasanni da sha’anin matasa na kasa, Sunday Dare ya bayyana wannan yayin kaddamar da majalisar da ke sa ido a kan aikin NYSC na kasa.

KU KARANTA: Minista ta hada-kai da banki sun sha kwana da $37m - EFCC

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministan ya na cewa:

“Domin nuna irin kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi ga sha’anin NYSC, shugaba Muhammadu Buhari ya amince a ba ‘yanuwan jinin mutane 10 da suka mutu yayin da su ke aikin NYSC.”

“Wadannan mutane sun rasu a rikicin zaben 2011 da ya barke a jihar Bauchi.” Inji Sunday Dare. A wancan lokaci Muhammadu Buhari ya sha kashi a zaben shugaban kasa.

KU KARANTA: Buhari zai ziyarci Borno domin kaddamar da wasu ayyuka

Ministan matasa da wasanni
Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Rahotan ya kuma ce Ministan wasanni da sha’anin matasan tarayyar ya yi na’am da kafa wata gidauniya ta musamman domin tallafa wa aikin yi wa kasa hidima.

Sunday Dare ya yi amfani da wannan dama ya bayyana tanadin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke yi a kan wannan tsari, ya ce gidauniyar za ta taimaka sosai.

Babu maganar soke shirin NYSC

Haka zalika Ministan ya ce NYSC na nan daram-dam-dam: “Za a cigaba da tsarin NYSC, ya zama cikin manufofin cigaba da zaman lafiya, matasa suna amfana matuka.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng