EFCC ta damke wasu Jami’ai 5 da ake zargi sun cinye fanshon tsofaffin Malaman Makaranta
- EFCC ta shiga kotu da Ma’aikatan Gwamnati a bisa zargin wawurar kudin fansho
- Wasu mutane biyar ake tuhuma da satar fansho da giratutin malaman makaranta
- Hukumar EFCC ta ce wadannan ma’aikata sun zare kudin Bayin Allah daga banki
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta gurfanar da wasu ma’aikata gwamnatin jihar Sokoto da laifin satar kudi.
Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin wadannan ma’aikata na hukumar da ke kula da fanshon ma’aikatan jihar Sokoto da wawurar N553, 985, 644.1.
An ware wadannan kudi ne da nufin biyan fansho da giratutin malaman firamare da suka yi ritaya.
KU KARANTA: Hukumar EFCC ta cafke tsohon Gwamnan jihar Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an da aka kama su ne: Abubakar Aliyu, Hassana Moyi, Haliru Ahmad, Kabiru Ahmad da kuma Dahiru Muhammad Isa
Wadannan mutane da ake zargi su na rike da mukaman sakatare, darektar kudi, mataimakiyar darektar kudi, akawu da kuma ma’aji na hukumar fanshon.
Shari’a a gaban kuliya
Punch ta ce an gurfanar da wadannan mutane ne a babban kotun jihar Sokoto, ana tuhumarsu da aikata laifuffuka 28, daga ciki akwai cin amana da satar kudi.
Laifuffukan da EFCC ta ke tuhumar mutanen da su, sun saba wa sashen dokokin 92 (2), 311 na final kwad, da sashen dokoki 351, 353, 348 na jihohin Arewa.
KU KARANTA: Zan hukunta duk wanda aka samu ya na taimakawa ‘Yan bindiga - Matawalle
Shugaban EFCC na shiyyar, Usman Bawa Kaltungo, ya ce ma’aikatan sun yi amfani da takardun bogi, su ka rika cire kudi a asusun fansho da giratutin ma’aikata.
Kaltungo yake cewa EFCC ta dauki mataki ne bayan wani cikin wadanda aka taba masu kudi ya kawo korafi, ya ce an saci N83.2m daga asusun kudin Bayin Allah.
Haliru da Kabiru sun cire N203,217,770.71 da N266,567,053 daga banki da sunan masu karbar fansho. A karshe, Alkali ya dage karar zuwa ranar 28 ga watan Yuni.
A baya kun ji jami’an AMCON da EFCC suna da’awar da iko da dukiyar gwamnati da aka sace, aka kuma yi nasarar karba a hannun wasu yaran Diezani Alison Madueke.
‘Yan Majalisa suna kokarin sasanta rikicin da ake yi tsakanin Jami’an Gwamnati idan AMCON ta ke cewa EFCC ta je ta karbe kayan da dama suna hannun bankuna.
Asali: Legit.ng