'Yan Majalisa sun ga ikon Allah, ana rigima kan dukiyar da yaran tsohuwar Minista suka sace

'Yan Majalisa sun ga ikon Allah, ana rigima kan dukiyar da yaran tsohuwar Minista suka sace

  • Wasu kadarorin sata da aka karbe daga hannun barayi ya jawo sabani
  • AMCON da EFCC duk suna da’awar cewa su za a damkawa kadarorin
  • Maganar sabanin ta kai gaban kwamitin bincike na Majalisar Tarayya

Kwamitin majalisar wakilan tarayya da ke bincike a kan kadarorin gwamnatin tarayya da aka sace daga 2002 zuwa 2020 ya gamu da abin mamaki.

Punch ta fitar da rahoto cewa wannan kwamiti ya shiga rudani a kan yadda zai sasanta hukumar EFCC da AMCON mai kula da kadarorin gwamnati.

Hukumar AMCON ta na ikirarin cewa ita ce ke da iko da wasu daga cikin kadarorin da ake zargin wasu na kusa da Diezani Alison-Madueke sun sace.

KU KARANTA: Minista ta hada-kai da banki sun sha kwana da wasu makudan kudi - EFCC

Wani ‘dan majalisa ya shaida wa jaridar cewa hukumar EFCC ta kawo korafi gaban kwamitinsu, ta na neman a hana AMCON taba wadannan dukiya.

An yi amfani da wasu daga cikin wadannan kadarori da aka karbe yanzu wajen cin bashin banki.

Wannan ‘dan majalisa da bai bari a ambaci sunansa ba, ya ce take-taken hukumar AMCON sun nuna tana neman karbe kadarorin daga hannun EFCC.

“EFCC ta na kukan cewa AMCON ta na neman karbe wasu kadarori da ta riga ta karbe daga hannun barayin gwamnati.” Inji ‘dan majalisar wakilan.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta zauna da Iyalan Hafsoshin Sojoji, IGP, DG DSS

'Yan Majalisa sun ga ikon Allah, ana rigima kan dukiyar da yaran tsohuwar Minista suka sace
Abdulrasheed Bawa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

AMCON ta ce kadarorin suna hannun bankuna a lokacin da hukumar EFCC ta karbe su. Bankuna sun karbi dukiyoyin ne domin su maida kudinsu da aka ci bashi.

Majiyar ta shaida mana cewa an karbe wadannan dukiya ne daga hannun irinsu Aluko da Omokore. "Bankuna sun karbe dukiyoyin daga hannun yaran Ministar."

Diezani Alison-Madueke ta rike kujerar Ministar man fetur a Najeriya, ana zargin ta da aikata rashin gaskiya a ofis, hakan ya sa ta bar kasar tun bayan zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng