Ana zargin karamin yaro ya yi garkuwa da kanwarsa, daga baya ya aika ta lahira

Ana zargin karamin yaro ya yi garkuwa da kanwarsa, daga baya ya aika ta lahira

  • Ana tuhumar wani yaro da laifin sace ‘yaruwarsa a Garin Dutsinma
  • Bayan an yi garkuwa da yarinyar, sai dai aka tsinci gawarta a daure
  • Magana ta kai gaban ‘yan sanda, ana zargin wani ‘danuwanta da laifi

Wata yarinya mai shekara uku a Duniya da aka yi garkuwa da ita a garin Dutsinma, jihar Katsina, ta rasu, Katsina Post ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Kamar yadda mu ka samu labari a jiya, ana zargin cewa wani ‘dauwan wannan Baiwar Allah mai suna Amina ne ya dauke ta, kuma ana zargin shi ya hallaka ta.

A ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, 2021, aka tabbatar da cewa wannan karamar yarinya ta bace, tun a lokacin ne aka rika yawo gida zuwa gida domin neman ta.

KU KARANTA: Mata 4,983 sun zama zaurawa a dalilin rikicin jihar Zamfara

Jaridar ta ce sai a makon nan ne aka ga gawar Amina a makwabta, an ajiye ta a kan wata kujera.

Katsina Post ta fahimci cewa wani ‘dan uwan marigayiyar na jini mai suna Aminu da wasu abokansa biyu ne ake zargi da laifin kitsa wannan danyen aiki.

Da aka yi hira da mahaifin Amina, Tukur Dan Ali, ya bada labarin yadda Aminu ya kawo masa takarda da sunan wasikar neman fansa daga hannun ‘yan bindiga.

Takardar da Aminu ya kawo ta nuna wadanda suka yi garkuwa da yarinyar suna neman N2m kafin ta fito, suka ce za su hallaka ta idan dai ba a kawo kudin ba.

Ana zargin karamin yaro ya yi garkuwa da kanwarsa, daga baya ya aika ta lahira
Gwamna Aminu Masari Hoto: www.fmic.gov.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Wani jirgin sama ya yi durar ungulu, ya ajiye mutane a Legas

Dan Ali ya kai takardar wajen jami’an ‘yan sanda, kuma an gayyaci wannan yaro wanda kamar ‘da yake a wurinsa, ya zo ya bada bayanin inda ya samu wasikar.

Ya ce: “Da mu ka shiga gidan, sai mu ka ji doyi, da mu ka kutsa sai mu ka gane inda warin ya ke fitowa, muna shiga sai ga gawar Amina a daure jikin wata kujera.”

An kai maganar zuwa babban ofishin ‘yan sanda, inda ake tuhumar Aminu da abokansa biyu.

A farkon makon nan ne aka ji Gidauniyar Attajirin Najeriya, Aliko Dangote Foundation ta tallafawa mata, inda mutane 10, 000 suka samu tallafi a jihar Bauchi.

Aliko Dangote ya batar da N10bn a Jihohi 13, mata 400, 000 a kauyuka sun ci moriyar wannan tsari. Gidauniyar ta na yin hakan ne domin fito mutane daga talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng