Dangote ya hada-kai da Gwamnati, ya raba N4.2bn domin ceto Mata 20, 000 daga talauci

Dangote ya hada-kai da Gwamnati, ya raba N4.2bn domin ceto Mata 20, 000 daga talauci

  • Gidauniyar Aliko Dangote Foundation ta rabawa Mata kudi a jihar Bauchi
  • Mata 20, 000 za a rabawa N10, 000 a kananan hukumomi 20 da ke Bauchi
  • Tsarin tallafawa marasa karfin Dangote ya ratsa jihohin Najeriya akalla 13

Jaridar This Day ta ce gidauniyar Aliko Dangote Foundation ta bada kudi har Naira biliyan 4.2 a matsayin tallafin da ke ba matan karkara a fadin Najeriya.

Gidauniyar ADF ta kan bada wannan tallafi ba tare da bada wani sharadi ba, da nufin ayi maganin talaucin da ake fama da shi a kauyukan da ke kasar nan.

Da yake magana wajen kaddamar da shirin wannan tallafi a Bauchi, Aliko Dangote, ya ce kawo yanzu mata marasa karfi 400, 000 sun amfana da tallafin.

KU KARANTA: Mun nemi mu biciki bidiyoyin Gandollar - Magaji Rimin-Gado

Rahoton Leadership ya ce Mansur Ahmed ne ya wakilci Alhaji Aliko Dangote a wajen wannan biki da aka yi a ranar 15 ga watan Yuni, 2021, a Bauchi.

A Bauchi, an soma raba Naira miliyan 200 ga mata 20, 000 da ke kananan hukumomi 30 da ke jiha, an raba wannan kudi ne da goyon-bayan gwamnati.

Mansur Ahmed a madadin Mai kudin nahiyar Afrikan, yake cewa gidauniyar Aliko Dangote Foundation ta ware Naira biliyan 10 da za a raba a fadin jihar.

Jihohin da aka raba wa mata tallafi

Gidauniyar ta yi irin wannan taimako ga marasa karfi a Legas, Kano, Jigawa, Kogi, Adamawa, Borno, Yobe, Niger, Nasarawa, Sokoto, Katsina da Kwara.

KU KARANTA: Bankin Duniya ta karyata Buhari, ta ce ya jefe mutum miliyan a talauci

Dangote ya hada-kai da Gwamnati, ya raba N4.2bn domin ceto Mata 20, 000 daga talauci
Aliko Dangote Hoto: www.bloomberg.com
Asali: UGC

A cewar Ahmed, a madadin Dangote, jihohin da aka tsara za a raba wa mata wannan kudin tallafi yanzu su ne: Osun, Edo, Ogun, Ribass, Anambra da Ebonyi.

“Tsarin tallafin ‘yan kudi ya na cikin manyan kudirorin tattalin arzikin gidauniyar Aliko Dangote Foundation, ana ba kowace mace N10, 000.” Inji Ahmed.

Gwamnati ta yabi Dangote, ta yi kira ga matan da suka samu tallafin, su yi amfani da kudin da kyau, tare da sa ran cewa ‘ya ‘yansu da ke gida za su amfana.

Idan za ku tuna, kwanaki an ji gidauniyar Bill Gates ta yi alkawarin kashe gudumuwar maganin COVID-19, Attajirin Duniyan ya ce zai kashe fam Dala miliyan 50.

Hakan na zuwa ne bayan an san ra'ayin Bill Gates shi ne Najeriya ba ta bukatar ta kashe makudan kudi wajen sayen rigakafi, ya ce zai fi kyau a inganta asibitoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel