Uwar-bari ta sa jirgin Birtaniya da ya kinkimo mutane zuwa Abuja ya canza hanya

Uwar-bari ta sa jirgin Birtaniya da ya kinkimo mutane zuwa Abuja ya canza hanya

  • Wani jirgin British Airways ya iso Najeriya, amma ya gaza sauka a garin Abuja
  • A karshe don dole wannan jirgin sama ya yi saukar gaggawa a filin jirgin Legas
  • Bayan jirgin saman ya yi ta yawo a iska, an sanar da direban cewa gari ya yi duhu

A ranar Talata, 15 ga watan Yuni, 2021, wani jirgin saman British Airways da ya dauka mutane daga kasar Turai ya yi maza ya sauka a filin Legas.

Sun News ta rahoto cewa wannan jirgi ya yi maza ya dura a filin sauka da tashin jirgin Murtala Muhammed bayan an shirya da zai sauka a Abuja.

Jaridar ta bayyana cewa jirgin ya sauka a garin Legas ne saboda yanayin gari bai bada a sauka a babban filin Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya ba.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga suna jin haza a hannun Sojojin sama da 'yan sanda

Jirgin saman ya iso filin sauka da tashin jirgin sama na Abuja, ya yi faman shawagi da kimanin karfe 5:00 na safe, a karshe aka ce ba zai iya sauka ba.

Saboda gudun ayi ganganci da ran jama’a, direban jirgin saman ya zabi ya sauka ta filin Legas.

Tribune ta ce saboda lokaci ya kure, ba a iya karasa wa da fasinjojin zuwa Abuja ba, don haka aka kama masu daki a otel a Legas kafin a samu wani jirgi.

Abin yi idan an samu matsala wajen sauka ko tashin jirgi

Dokar tukin jirgi a Najeriya ta bada dama ga direbobi su saki hanya, su sauka a wani filin jirgin saman idan har sun ga cewa sauka a inda suke so zai yi wahala.

British Airways
Jirgin British Airways Hoto: www.brandessencenigeria.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Saura kiris da na mutu a jirgin COAS - Hon. Namdaz

Haka zalika ana yi wa ma’aikatan jirgi horon musamman domin su san matakan rigakafi da za su dauka idan har an samu irin wannan yanayi a samaniya.

Babban jami’in da ke kula da aikin jiragen British Airways a kasashen Najeriya da Ghana, Adetutu Otuyalo, ya ce yanayin gari ne ya sa jirgin ya gaza sauka.

A daidai wannan lokaci kuma mun ji cewa fasinjojin da suka saye tikiti domin zuwa Landan daga Abuja, sun zauna carko-carko, jirginsu bai samu tashi ba.

A baya kun ji an bada umarnin sauke tutoci a dukkan gine-ginen gwamnati na kwanaki uku saboda mutuwar hafsun sojin kasa da wasu jami'an sojoji.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki wannan mataki ne domin karrama marigayi Janar Ibrahim Attahiru da sauran sojoji 10 da suka rasu a hatsarin jirgi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng