Sojojin Najeriya sun yi wa Miyagun da ke ta’adi a Jihohin Arewa luguden wuta

Sojojin Najeriya sun yi wa Miyagun da ke ta’adi a Jihohin Arewa luguden wuta

  • Sojoji da ‘Yan Sanda sun shiga jeji, suna ta yi wa ‘Yan bindiga aman wuta
  • Jami’an tsaro sun lallasa ‘Yan bindiga a irinsu Katsina, Benuwai, Sokoto
  • Rahotanni sun ce ana kara baza jami’an ‘yan sanda zuwa yankin Zamfara

Jaridar Punch ta ce akwai alamun da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun shiga yin barin wuta a mafakokin ‘yan bindiga a wasu yankunan Arewacin kasar nan.

Wasu manyan jami’an sojoji sun shaida wa jaridar cewa sojoji sun soma ragargazar ‘yan bindiga a Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya da jiragen sama.

Rahoton ya ce an kai wa ‘yan bindigan farmaki a jihohin Benuwai da Katsina, kuma ana sa rai cewa nan ba da dade wa za a auka wa sauran jihohin da ke yankin.

KU KARANTA: An tantance sabon shugaban hafsun sojan kasa a Majalisa

Ana kai farmaki a Katsina

A jihar Katsina, sojojin sama da ‘yan sanda suna cigaban da bankado ‘yan bindiga a Batsari, Jibia, Sabuwa, Danmusa, Safana, Matazu, Kankara, da kuma Dandume.

Haka zalika jami’an tsaron sun shiga garuruwan Dutsin-ma, Kurfi da Faskari inda wadannan miyagu sun dade suna addabar manoma da sauran mutanen karkara.

Wani jami’i ya ce: “Mu na kai hari, mu gano inda ‘yan bndiga suka labe a kusan kowane yanki na jihar.”

Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da cewa dakarun da ke jihar suna bakin kokarin kawo zaman lafiya.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta rugurguza wasu coci a Legas

Sojojin Najeriya sun yi wa Miyagun da ke ta’adi a Jihohin Arewa luguden wuta
Hafsun Sojojin Najeriya Hoto: @FemiAdesina
Asali: Facebook

Operation Whirl Stroke ta kai hare-hare

Kamar yadda mu ka samu rahoto a yau, Rundunar Operation Whirl Stroke ta shiga Taraba, Nasarawa da Benuwai, ta na lallasa ‘yan bindigan da su ka fake a jeji.

“Mun kai farmaki a yankin Sankera a Benuwai. Shiyasa manoma za su iya komawa gidajensu, su fara shirin aikin gona.” Wani jami’in tsaro ya tabbatar wa 'yan jaridar.

A Sokoto, ‘yan sanda sun shiga Sabon Birni, Isa, Rabah da Goronyo, su na nemen ‘yan bindiga. A Zamfara kuwa, ana kara baza ‘yan sanda zuwa inda babu zaman lafiya.

A jiya kun ji cewa Ministan sufuri, Royimi Amaechi, ya bayyana abin da zai faru da Hadiza Bala Usman bayan an yi waje da ita daga kujerar shugabar hukumar NPA ta kasa.

Rotimi Amaechi ya fada wa 'yan jarida cewa suna zuzuta lamarin, ya ce: "Ban isa in dakatar da Hadiza daga ofis ba, Shugaban kasa Buhari ne kadai ya ke da wannan iko."

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng