Gwamnatin Tarayya ta yi sammako, ta ruguza coci, lamarin ya na neman jawo abin magana

Gwamnatin Tarayya ta yi sammako, ta ruguza coci, lamarin ya na neman jawo abin magana

  • Gwamnatin Tarayya ta share wasu coci da aka gina ba tare da izini ba a Legas
  • Ma’aikata sun duro da asuba, suka shiga rusa cocin yayin da mutane suke barci
  • Hukuma ta ce tun farko an tada ginin wadannan coci ne ba da amincewarta ba

Rahoto daga jaridar nan ta Punch ya nuna cewa ana ta ce-ce-ku-ce a dalilin rusa wasu coci 12 da aka yi a unguwar 2nd Avenue, FESTAC da ke garin Legas.

Jami’an hukumar harkokin gida ta tarayya sun yi aikin da ya jawo surutu bayan sun ruguza wasu coci da ake ibada da aka ce an gina a kan filayen haramun.

Ma’aikata sun dura wannan unguwa tun karfe 5:00 na safe, ba su gama wannan aiki ba sai 3:00 na yamma, hakan ya faru ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Legas ta amince a bude Masallatai da Coci

Wajen ruguza wadannan coci, abin har ya kai an rusa wata kasuwa da wani shagon saida motoci. Wadanda lamarin ya shafa suna kukan cewa an zalunce su.

Shugaban cocin Gate of Righteousness Evangelical Int’l, Joshua Obong ya ce ya gina cocinsa ne shekaru 18 da suka wuce, don haka babu dalilin ruguje shi.

Fasto Obong yake cewa an rusa masa wurin ibada ba tare da an kawo masa wata takarda ba. Hakan ya zo lokacin da ake yajin-aiki a kotu, aka gaza kai kara.

Har ila yau an ruguza cocin Christ Gospel Church International, shugaban wannan coci, William Ehiorenren, ya ce sun yi magana har an yarda a dakatar da aikin.

KU KARANTA: An garkame wasu coci da Masallatai 8 a jihar Legas

Gwamnatin Tarayya ta yi sammako, ta ruguza coci, lamari ya na neman jawo abin magana
Wani Coci a Legas Hoto: www.thenationonlineng.net
Asali: UGC

William Ehiorenren ya ce sun dade suna bautar Ubangiji a wannan wuri, sai rana daya kurum aka zo aka fatattake su, domin a saida filayen, a samu kudin shiga.

Faston ya ke cewa: “Mun ji suna so su karbe filayen ne, su saida wa Attajirai, su samu kudi. Ban taba ganin inda aka ba mutane kwana bakwai su tattara kayansu ba.

A cewar Politics Nigeria, ana zargin wadannan mutane sun share bola ne sun daura ginin coci, sun yi shekaru tsakanin 13 zuwa 20 a haka, ba da iznin hukuma ba.

Dazu mu ka ji cewa Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya na ganin ya kamata a karawa Gwamnoni karfi, sannan kuma a rusa kananan hukumomi a Najeriya.

David Umahi ya na so a samu mataimakan shugaban kasa shida ta yadda kowane yanki zai samu, sannan an ji Umahi ya na cewa PDP ce ta shuka irin rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel