Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokubo

Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokubo

- Shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra kuma tsohon kwamandan tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo yayi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo

- Mujahid Asari Dokubo ya zargi Nnamdi Kanu da waskar da kudaden Biafra zuwa aljihunsa inda har ya zargesa da masa karyar karbar miliyan 20

- Dokubo ya sha alwashin kai Nnamdi Kanu kasa tare da ceto Ibo da suke fadawa tarkon Kanu wanda yace ya mayar da Biafra kasuwanci

Mujahid Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru kuma shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra, ya kwatanta shugaban IPOB da zama dan ta'adda.

A wani bidiyo da ya saki a kafar sada zumunta, Dokubo ya zargi Kanu da amfani da fafutukar Biafra a matsayin wani nau'in kasuwanci.

Ya zargi Kanu da waskar da kudaden da za a yi amfani dasu domin kafa Biafra, Daily Trust ta ruwaito.

"A yanzu ce mana suke haka Indiya, Rasha da sauransu suke adana kudade. Haka Biafra zata zama karkashin shugabancin dan ta'adda Nnamdi Kanu."

KU KARANTA: Da duminsa: Ban gamsu da tattalin arzikin kasar nan ba, Buhari

Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokubo
Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokubo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari

"Sun yi ikirarin cewa sun kawo mun kudi N20 miliyan har Cotonou. Muna jiransu su kawo shaida. Sun zo Cotonou kuma na hadu dasu har na basu masauki. Babu sisi da suka kawo."

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, Dokubo ya ce, "Me yasa Ibo suka bar dan damfaran nan yake damfararsu? Ibo, dole ne ku tashi tsaye. Yana so ya tarwatsa Onyeama da Ekweremadu. Yana so ya tarwatsa kowa kuma Ibo sun yi shiru.

“Biafra taku ce, baku da wata hanyar samu. Abun takaici ne yadda Ibo suka fada tarkon wannan shaidanin, amma lokaci yayi.

"Na fito domin ku, kuma zan samo ku. Na ce a bar jama'armu su yi zabe amma sai ka turo min karnukanka.

"Nnamdi Kanu ni ba sa'anka bane a nan, babu shakka sai na kai ka kasa. Zan tarwatsa wannan gagarumar shaidaniyar daular da ka kafa take hana mu samun Biafra."

Har a halin yanzu Kanu bai yi martani kan wannan zargin da Dokubo yake masa ba.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammaadu Buhari yace masu daukar nauyin ta'addanci a kasar nan suna neman dacewa ne. Shugaban kasan ya sanar da hakan a ranar Juma'a yayin tattaunawa da gidan talabijin na kasa (NTA).

Buhari ya ce duk wanda aka kama da hannu cikin daukar nauyin ta'addanci a kasar nan zai dandana kudarsa kuma dole ne ya fuskanci shari'a.

Ya ce da yawa daga cikin masu daukar nauyin ta'addanci mutane ne masu kudi da kuma wadanda a halin yanzu basu cikin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng