Gwamnan APC ya kawo shawarar a rika nada Mataimakan Shugaban kasa 6 a Najeriya

Gwamnan APC ya kawo shawarar a rika nada Mataimakan Shugaban kasa 6 a Najeriya

  • David Umahi ya na so a samu mataimakan shugaban kasa 6 ta yadda kowane yanki zai natsu
  • Gwamnan jihar Ebonyi ya na ganin sauya fasalin tsarin mulki zai kawo karshen rikice-rikice
  • A na sa ra’ayin, ya kamata a soke kananan hukumomi, a karawa Gwamnonin jihohi karfin iko

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kawo shawarwari game da yadda za a shawo kan matsalolin da ake fama da su a halin yanzu a kasar nan.

Da aka yi hira da gwamna David Umahi a Channels TV a ranar Litinin, ya ce za a samu saukin rikici da zaman lafiya idan har aka sake fasalin kasar nan.

Gwamna David Umahi ya na ganin cewa rikici zai ragu idan kowane yanki daga cikin yankuna shidan da ake da su ya samu mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA: Borno ta na more romon damokaradiyya, Zulum ya yi manyan ayyuka 550

Jaridar The Cable ta rahoto gwamnan ya na ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa jihohi karfi, hakan na nufin a rage ikon gwamnatin tarayya.

Ya ce: “Ina da ra’ayi na dabam game da kiraye-kirayen sauya fasalin kasa da ake yi, abin da zan ba Muhammadu Buhari shawara shi ne, a kara karfin jihohi.”

“An bada shawarwari masu ma’ana, a samar da mataimakan shugaban kasa shida a kasar nan.”

“Kowane mataimakin shugaban kasa ya fito daga bangare guda. Tashin hankali zai ragu.” Dave Umahi ya kara da: “Wannan ya na da matukar muhimmanci.”

KU KARANTA: Ganduje ya yi magana a game da lokacin da zai ajiye siyasa

Gwamnan APC ya kawo shawarar a rika nada Mataimakan Shugaban kasa 6 a Najeriya
Gwamna David Umahi Hoto: www.thenationonlineng
Asali: UGC

Umahi ya kawo wata magana: “Zan bada shawarar sake tsarin shugabanci ta yadda za a kirkiri kananun tarayya–a ba jihohi karfi, a soke karamar hukuma."

Jaridar Daily Post ta rahoto gwamnan har ila yau ya na ikirarin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi wa Kudu maso gabas abin da PDP ta gagara yi.

A game da rashin tsaro kuwa, gwamnan na Ebonyi ya bayyana cewa tun a lokacin mulkin PDP aka shuka matsalar, sai yanzu ne ta fara tsiro har ta yi ‘ya ‘ya.

Idan mu ka shiga batun rashin tsaro, za ku ji cewa bincike ya nuna an yi awon-gaba da daliban makaranta 936 daga watan Disamban shekarar 2020 zuwa yau.

‘Yan ta’addan Boko Haram da ‘Yan bindiga su na yi wa harkar ilmin Boko barazana. Jihohin da suka fi fuskantar hadari su ne: Zamfara, Kaduna, Neja da Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel