An garkame Coci coci da Masallatai guda 8 a jahar Legas
Gwamnatin jahar Legas ta sanar da rufe wasu masallatai da coci coi guda 8 a fadin jahar saboda karya dokokin kiyaye muhalli, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito.
Shugaban hukumar kiyaye muhalli na jahar Legas, Dakta Dolapo Fasawe ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace gwamnati ta dauki matakin garkame wuraren bautan ne saboda kare jama’a daga hatsarin kiwon lafiya.
KU KARANTA: Kaico! Wata mahafiya ta kashe ‘ya’yanta mata guda 2 a jahar Imo
Shugaban yace babu batun daga kafa ga duk wuraren bautan da ke kokarin yi ma dokar kare muhalli karan tsaye, don haka gwamnati za ta dauki mataki a kan duk wanda ya karya dokan ba tare da la’akari addini ba.
Wuraren bautan da aka kulle sunan nan ne a: 68, Old Ota Road, Orile Agege; 4, Ademola Oshinowo Street, Off Love Street, Ketu; 1 Dele Amuda Street, Lekki, 17, Ajileye Street, Ilaje Bariga; 39, Kusenla Road, Elegushi and Ajayi Bembe Street Abule Oja, Yaba, da sauransu.
“Duk wasu wuraren bauta dake damun jama’a da hayaniya zasu fuskanci hukuncin doka, duk da cewa gwamnati na girmama addinai, ba za ta lamunci tauye hakkin jama’a da sune addinai ba. Hukumar ta sha samun korafe korafe daga jama’a game da yadda wuraren bauta suke cutar dasu.
“Duk gargadin da muka ma wuraren bautan nan basu ji ba, don haka gwamnati ta damu da yadda jama’a ke tafiyar da addinansu ba tare da sun cutar da sauran jama’a ba.” Inji shi.
A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Imo ta sanar da kama wata mata mai suna Ukamaka Ezike wanda ake zarginta da kashe ‘ya’yanata mata guda biyu masu kananan shekaru.
A cewar mahaifin yaran, Christian, yace baya gari a ranar 15 ga watan Nuwamba, a wannan lokaci ne matarsa ta lakada ma yaransu uku dan banzan duka. Yaran sun hada da Kosarachukwu mai shekaru 4, Chinwendu mai shekaru 2 da Chinecherem yar wata biyu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng