Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Legas ta amince a bude Masallatai da Coci-coci
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa ya amince da fara bude wuraren bauta daga ranar Juma'a 19 ga Yuni, 2020.
Ya ce za'a fara da Masallatai ne ranar 19 ga Yuni yayinda za'a fara bude coci-coci ranar 21 ga Yuni, 2020.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayinda yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Marina.
Mai magana da yawun gwamnan, Gboyega Akoshile, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis
Yace: "Coci-coci da Masallatai zasu koma ayyukansu a Legas kamar haka:
1. Musulmai za su fara ranar 19 ga Yuni yayinda Kiristoci zasu fara ranar 21 ga Yuni, 2020.
2. Ba'a amince kananan yara masu kasa da shekaru 15 da haihuwa su halarta ba
3. Ranar Juma'a da Lahadi ne kawai aka amince a bude
TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng