Saboda na bukaci ayi gaskiya a NPA, Hadiza Bala Usman ta sa aka yi waje da ni inji Sanata

Saboda na bukaci ayi gaskiya a NPA, Hadiza Bala Usman ta sa aka yi waje da ni inji Sanata

- Binta Masi Garba ta zargi Hadiza Bala Usman da yin waje da ita a majalisar NPA

- Sanatar ta ce shugabar NPA ta sa aka sallame ta saboda ta binciko wasu abubuwa

- Garba ta ce Bala Usman ta yi wa Shugaban kasa da Ministan sufuri rashin kunya

Sanata Binta Masi Garba, tsohuwar ‘yar kwamitin da ke sa ido a aikin hukumar NPA, ta bada labarin yadda su ka yi da Hadiza Bala Usman.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Binta Masi Garba ta na zargin Hadiza Bala Usman da sa wa ayi waje da ita bayan ta bukaci ayi gaskiya a hukumar NPA.

A wani jawabi da tsohuwar Sanatar ta yankin Adamawa ta Arewa ta fitar, ta zargi Hadiza Bala Usman da aka dakatar da saba wa umarnin manya.

KU KARANTA: Ana zargin Bala Usman da fifita kamfanin Dangote a tashar Onne

Sanata Garba ta ce Hadiza Bala Usman ta rika yi wa shugaba Muhammadu Buhari da ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, abin da ta ga dama.

Tsohuwar ‘yar majalisar dattawar Najeriyar ta ce hankalinta bai kwanta a kan yadda Bala Usman ta jagoranci hukumar NPA a lokacin da ta ke ofis ba.

“A Junairun 2021, aka cire ni da Sanata John Akpanudoedehe daga majalisar da ta ke sa ido a kan aikin NPA, kuma shakka babu, Hadiza Bala Usman da aka dakatar ce ta shirya yadda aka yi waje da mu.”

“Na saba nuna rashin kwanciyar hankalina a kan yadda shugabar ta ke jagorantar wurin nan, ba na shakkar cewa hakan ya sa ta yi kokarin ganin an cire ni daga majalisar da ke kula da NPA.”

KU KARANTA: Mutane su ka nuna suna so a kara Masarautu a Kano inji Ganduje

Saboda na bukaci ayi gaskiya a NPA, Hadiza Bala Usman ta sa aka yi waje da ni inji Sanata
Sanata Binta Masi Garba
Asali: UGC

“A sani cewa, an tsige ni daga majalisar ne ba tare da sanin Ministan sufuri ba, wanda ba kasafai aka saba yin hakan ba.” Inji Binta Masi Garba.

Masi Garba take cewa ta gano akwai haka-da-haka game da yadda NPA ta ke batar da kudi, don haka ta gabatar da wasu tambayoyi, amma aka ki ba ta amsarsu.

A cewar Sanatar, ta so ta ajiye aikinta, amma aka ba ta shawarar ka da ta yi hakan. Amma ta ga Usman ta na ta nuku-nuku, ba ta jin dadin yadda ta saka mata ido.

Kwanaki aka ji cewa an dakatar da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa a Najeriya, NPA, Hadiza Bala Usman, domin hakan ya bada damar ayi bincike a kan ta.

A wata wasika da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ana karkatar da kudin da ya kamata ace NPA ta dawo da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng