2023: Shugaba Buhari ya yiwa Bola Tinubu hannunka mai sanda

2023: Shugaba Buhari ya yiwa Bola Tinubu hannunka mai sanda

  • Jam'iyyar APC zata yanke shawara akan zabe mai gabatowa,bayan tayi dubi da idon basira
  • Buhari ya ce akwai kwamiti da zasuyi wanan aiki bawai haka nan,wanda ya kamata da wanda bai kamata ba su dinga tsoma baki
  • Ana hasashen Mista tinubu da son karbar ragamar mulkin Nijeria a zabe mai gabatowa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce shawarar da jam’iyya mai mulki ta APC ta yanke game da shugabancinta da kuma zaben 2023 zai kasance daga masu alhakin haka,ya kuma ki cewa uffan kan ko ragamar mulki zai koma yankin kudancin kasar.

Ya ce jam'iyyar za ta yanke hukunci ne tare da mambobin jam'iyyar, ba kamar yadda kowa ke tsoma baki ba "kawai mutum na kwance a Lagos", wanda yar manuniya ta hasko cewa tsohon Gwamnan Legas ne Bola Tinubu.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

Shugaba Buhari yayi jawabi
2023: Shugaba Buhari ya yiwa Bola Tinubu hannunka mai sanda Photo: President Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

Mista Tinubu ana hasashen cewa yana kwadayin shugabancin kasa a 2023 kuma ya shiga gwagwarmaya don mulkan jami'yyar APC.

Shugaban ya yi wannan tsokaci ne lokacin da yake hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis.

An yi masa tambaya a kan wani yanki ne na kudu APC za ta mara wa baya don ta mallaki shugabancin kasar idan ya bar mulki a 2023.

A cikin martanin nasa, Buhari bai ce komai ba game da batun sauya sheka amma ya ba da amanna cewa jam'iyya ne zata yanke shawara.

Sannan ya yi magana game da tsarin yanke shawara tun daga kasa har sama, wanda a cewarsa zai baiwa mambobin damar tunani da kansu.

Tun a shekarar 2015 lokacin da APC ta hau mulki, Mista Tinubu ya ci gaba da fuskantar kalubale daga wasu shugabannin jam’iyyar, tare da hana shi rike madafan ikon jam’iyyar.

A bangare guda, mambobin iyalin marigayi MKO Abiola, sun nuna rashin jin daɗin su kan yadda gwamnati tayi watsi da al'amuransu.

Mai magana da yawun gidan, Rahaman Abiola, shine ya bayyana haka ranar Asabar 12 ga watan Yuni, a jihar Ogun, yace gwamnati ta kasa cika musu alƙawarin da tayi musu a shekarun baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Da yake magana a Abekuta, babban Birnin jihar Ogun, Abiola yace har yanzun iyalan gidan su basu amfana da komai ba daga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel