Talauci: Boko Haram na jan hankalin jama'a da N5,000 ko N10,000, Zulum

Talauci: Boko Haram na jan hankalin jama'a da N5,000 ko N10,000, Zulum

- Gwamna Zulum na jihar Borno ya bayyana yadda 'yan Boko Haram ke bada 5,000 zuwa 10,000 ga masu musu leken asiri

- Kamar yadda ya bayyana suna bada kudaden ga wasu masu tallafa musu wurin safarar makamai

- Zulum ya tabbatar da cewa dole ne a tsamo jama'a daga talauci idan ana son dakile wannan lamarin

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce 'yan ta'addan Boko Haram suna baiwa mutane N5,000 zuwa N10,000 domin su zama masu kai musu bayanai ko kuma yi musu safarar makamai.

Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin jawabin ranar damokaradiyya da kuma bikin tunawa da ranar da ya hau karagar mulkin jihar Borno.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Zulum yace akwai bukatar shawo kan matsalar talauci a kasar nan inda ya jajanta yadda 'yan ta'addan cikin sauki suke jan mutane zuwa kungiyarsu.

KU KARANTA: A lokacin da aka kwatanta mu da birai, Twitter ta ki goge wallafar, Lai Mohammed

Talauci: Boko Haram na jan hankalin jama'a da N5,000 ko N10,000, Zulum
Talauci: Boko Haram na jan hankalin jama'a da N5,000 ko N10,000, Zulum. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Zulum ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta samu manyan nasarori a fannin cigaba a jihar kuma tare da bada tsaro ga jama'ar yankin daga hare-haren Boko Haram.

"Mun gano cewa akwai lokutan da 'yan ta'adda ke baiwa masu kai musu bayanai 5,000 zuwa 10,000 tare da masu musu safarar makamai," yace.

"Akwai bukatar mu tabbatar da cewa 'yan kasarmu suna da goyon bayan da suke bukata, ba tare da an turasu ga halaka ba ko kwadayin dan abinda 'yan ta'adda zasu basu.

“Akwai yuwuwar 'yan ta'adda zasu iya bada abinci da kudade domin su janyo hankalin mutane su shiga suna kai musu bayanan yankunansu."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa yayi kokari tun bayan da suka hau karagar a 2015.

Buhari ya sanar da hakan ne a tattaunawa ta musamman da yayi da gidan talabijin na kasa (NTA) a ranar Juma'a.

Shugaban kasan ya bukaci 'yan Najeriya da su dinga yi wa mulkinsa adalci idan suka tashi yanke hukunci. Ya kara da cewa jama'a su dinga duba abinda ya samar a mulkinsa da kuma abinda akwai kafin ya hau karagar jagorancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel