Bayan shafe awa 10 ana kus-kus, Dattawan Najeriya za su sa labule da Shugaba Buhari

Bayan shafe awa 10 ana kus-kus, Dattawan Najeriya za su sa labule da Shugaba Buhari

  • Sarkin Musulmi da John Cardinal Onaiyekan sun kira wani taro a Najeriya
  • Tsofaffin Shugabanni, jagororin addini da wasu Sarakuna sun samu halarta
  • Babu wanda ya yi wa ‘yan jarida magana bayan an tashi daga dogon zaman

Manyan jagororin addini a Najeriya a karkashin Sultan, Muhammad Sa’ad Abubakar III da John Cardinal Onaiyekan sun jagoranci wani zama na musamman.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa bayan kammala wannan zama da aka shafr kusan sa’o’i goma, babu wanda ya yi wa manema labarai magana a ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce an soma zaman ne da kimanin karfe 11:30 na safe, ba a tashi ba zai 8:20 na yamma.

KU KARANTA: Makiyaya ba su rike makamai, iyakarsu sanduna - Buhari

Emeritus John Cardinal Onaiyekan ne kadai ya iya cewa: “Mun tattauna a kan komai.” Shi kuwa Hakeem Baba Ahmed cewa ya yi bai samu iznin magana ba.

Kafin a soma taron da aka shafe sa'o'i goma ana yi, wadanda suka kira taron sun ki barin ‘yan jarida su halarci zaman, suka ce taron ba na ‘yan jarida ba ne.

Wadanda suka halarci wannan zama a Transcorp Hilton da ke Abuja sun hada da Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar, da shugaban kungiyar NLC.

Sannan an ga tsohon AGF, Kanu Agabi, Sakatare Janar na kungiiyar CAN, Joseph Daramola, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya, da tsohon Ministan noma, Dr. Audu Ogbe.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata da Yara, sun harbe Dalibai a Zaria

Shugaba Buhari da Osinbajo
Shugaba Buhari da Mataimakinsa, Osinbajo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ragowar manyan sune Oonin Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor da na Afenifere Cif Ayo Adebanjo.

Punch ta ce za a dauki rahoton wannan zaama da aka yi, a kai gaban shugaba Muhammadu Buhari.

A ranar Juma’a ne ake sa ran wadannan manyan mutane za su hadu da shugaban Najeriya a fadar Aso Villa. Idan sun gana, za su fadakar da shi a kan zaman na su.

Dazu kun ji labari daga fadar shugaban kasa cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa 'yan kasa jawabi na musamman a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni 2021.

A gobe ake bikin tunawa da zaben 12 ga watan Yunin 1993, wanda gwamnatin soja ta soke. Gwamnatin Buhari ta zabi wannan rana domin tunawa da damukaradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng