Buhari: 'Yan Najeriya akwai mantuwa, har wadanda ake zargi da rashawa cin zabe suke

Buhari: 'Yan Najeriya akwai mantuwa, har wadanda ake zargi da rashawa cin zabe suke

- Shugaba Muhammadu Buhari yace 'yan Najeriya suna da mantuwa tunda hatta wadanda ake zargi da rashawa sun zabe

- Ya bayyana cewa wannan mulkin da yake ba na soja bane, na damokaradiyya ne kuma shi ya baiwa wadanda ake zargi damar cigaba da siyasa

- Buhari yace akwai abun mamaki idan ka ga yadda wasu wadanda aka zaba ke watanda da dukiyar gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu ya ce 'yan Najeriya suna da mantuwa ganin yadda hatta wadanda ake zargi da rashawa ke cin zabe.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na kasa (NTA).

Buhari yace ya kasance a gaba-gaba wurin yaki da rashawa tun a lokacin yana soja, ya kara da cewa damokaradiyya ce ta bada dama hatta ga wadanda ke cin rashawa su cigaba da zama a tsarin siyasa.

"A lokacin da nake da yarinta, cikin khaki, da nazo na kama shugaban kasa, mataimakinsa, gwamnoni, ministoci, kwamishinoni sannan na tsare su. Nace suna da laifi har sai idan zasu iya wanke kansu. Amma a yanzu damokaradiyya ce," yace.

KU KARANTA: Boko Haram da 'yan bindiga sun yi min barazana sama da sau 100, DCP Abba Kyari

Buhari: 'Yan Najeriya akwai mantuwa, har wadanda ake zargi da rashawa cin zabe suke
Buhari: 'Yan Najeriya akwai mantuwa, har wadanda ake zargi da rashawa cin zabe suke. Hoto daga bashir Ahmad
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tsawon shekaru 6, mata da 'ya'yanta na kwana a bandaki bayan mijinta ya tsere

"Mun kafa kwamitin bincike, amma har da yanayin yankunanmu. Ga wadanda ke da mukami kuma sabooda doka ce bayyana dukiya yayin da suka zama gwamnoni, ministoci ko kwamishinoni, an bincikesu.

"Ga wadanda ba zasu iya bayyana sauran dukiyoyinsu ba ko kuma kudadensu na banki, mun bukaci da su miko su. Daga bisani an kama ni tare da tsare ni kuma an basu dukiyoyinsu. Toh wannan ce Najeriya.

"'Yan Najeriya suna da mantuwa. Ina farin ciki idan na tuna mafi yawan 'yan Najeriya suna ganin yadda wannan mulkin ke kokari. Amma jama'a na watanda da kudi, da yawansu an zabesu ne a matakin jiha ko tarayya kuma jama'arsu na mutunta su.

“Zaku iya zarginsu saboda ko lokacin da aka zabesu, gida daya garesu amma yanzu suna da su a Abuja da Legas. Amma idan ka duba halastaccen albashinsu da nauyin dake kansu, zaku sha mamaki."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai gamsu da yadda tattalin arzikin kasar nan yake tafiya ba.

Buhari, wanda ya sanar da hakan a tattaunawa ta musamman da yayi da NTA, ya kara da cewa mulkinsa na aiki tukuru wurin ganin ta janyo masu zuba hannayen jari kai tsaye a Najeriya.

"Ban gamsu da yanayin tattalin arziki ba. Hakan ne yasa nake ta janyo kasashen ketare domin basu damar amincewa tare da zuba hannayen jari a Najeriya. Hakan ne zai samar da aikin yi," yace.

Najeriya ta fita daga mugun yanayi na karayar tattalin arziki wanda ta kwashi shekaru 33 bata shiga kamarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel