Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya misalin karfe 7 da safen nan

Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya misalin karfe 7 da safen nan

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi na musamman ga yan Najeriya da safiyar Asabar, 12 ga watan Yuni, fadar shugaban kasa ta bayyana haka.

A jawabin da Femi Adesina, mai magana da yawun Buhari ya saki ranar Juma'a a Facebook, ya bayyana cewa Buhari zai yi wannan jawabi ne don murnar zagayowar ranar Demokradiyya.

A cewarsa, za'a haska jawabin misalin karfe 7 na safe.

"Domin murnar ranar Demokradiyya, 12 ga Yuni, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga kasa ranar Asabar, 12 ga Yuni, 2021, da karfe 7 na safe," Adesina yace.

"Ana kira ga gidajen Talabijin, gidajen Rediyo da sauran kafafen yada labarai su haska daga tashar NTA da Rediyo Najeriya."

Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya gobe
Da duminsa: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya gobe
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel