An harbe Dalibai, an yi awon-gaba da mutane rututu daga Nuhu Bamali Polytechnic cikin dare

An harbe Dalibai, an yi awon-gaba da mutane rututu daga Nuhu Bamali Polytechnic cikin dare

‘Yan bindiga sun yi ta’adi a Makarantar Nuhu Bamali da ke garin Zaria jiya

An harbe ‘daliban makarantar biyu, daya cikinsu ya mutu a hanyar asibiti

Wasu daga cikin wadanda aka sace sun dawo, wasu biyu suna nan a tsare

Rahotanni daga mabanbantan wurare sun tabbatar mana da cewa ‘yan bindiga sun shiga makarantar koyon aiki ta Nuhu Bamali ta Zaria, Kaduna.

A ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, 2021, wasu mutane da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne sun kai wa mutanen makarantar hari da dare.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto da safen nan cewa har yanzu ba a san adadin mutanen da aka tafi da su ba, amma tabbas an yi gaba da mutane da dama.

KU KARANTA: 'Yan Sanda yi ram da wadanda su ka kona gidan Gwamnan Imo

Daga cikin malaman makarantar da aka sace akwai Mista Habila Nasai da Malam Adamu Shehu Shika wanda yake koyawar a sashen karantar da ilmin akawu.

An harbi wani dalibin makarantar wanda ya mutu yayin da ake kokarin kai shi zuwa asibiti.

Jami’in yada labarai na makarantar ta Nuhu Bamali Polytechnic, Malam Abdallah Shehu ya tabbatarwa manema labarai aukuwar lamarin dazu nan da safe.

Sai dai Abdallah Shehu bai iya yi wa ‘yan jarida cikakken bayani game da abin da ya wakana ba. Haka Punch ta samu labarin, amma ba tare da cikakken bayani ba.

Majiyoyinmu sun tabbatar mana da cewa an yi garkuwa da wasu malamai da ma’aikatan makarantar, cikin dalibai biyu da aka harbe, daya yana jinya yanzu.

KU KARANTA: Yan Bindiga sun kashe mutum 5 a hanyar Zaria

Nuhu Bamalli Poly
Makarantar Nuhu Bamali Polytechnic Hoto: www.punchng.com
Asali: UGC

‘Yan bindigan sun tsere da iyalin wani Malami mai suna Ahmad Abdul da yake koyarwa a sashen lissafi, an dauke matarsa da kuma ‘ya ‘yansa biyu a gidansu.

Labarin da muke samu daga baya shi ne an fito da ‘ya ‘ya da mai dakin wannan malami yau da safe. Makarantar ta na nan a hanyar Kaduna zuwa garin Zaria.

Akalla yaran makarantar uku ake tunanin an tafi da su. Har yanzu ba a iya tabbatar da sunayensu da sashen karatunsu ba, An bada sunan wanda ya mutu da Ahmad.

Idan ba ku manta ba, a ranar Alhamis ne aka ji shugaban Sojojin Sojan kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya soma tankada da rairaya makonni biyu bayan ya shiga ofis.

An yi canji a gidan sojan kasa, inda kakakin sojoji zai bar ofis, aka nada Onyema Nwachukwu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel