Sunayen biranen duniya mafi muni da za a iya rayuwa a 2021, Legas ce ta biyu

Sunayen biranen duniya mafi muni da za a iya rayuwa a 2021, Legas ce ta biyu

Rahoton da sashen binciken sirri na tattalin arziki na 2021 na duniya ya fitar ya bayyana garin Legas a matsayin birni na biyu mafi muni da dan Adam zai iya rayuwa a duniya.

Rahoton da legit.ng ta gani ya nuna cewa birnin Damascus, babban birnin Syria ya zama birni mafi muni da dan Adam zai iya rayuwa a duniya.

Kamar yadda rahoton ya nuna, birane 140 a fadin duniya ne aka duba kuma an yi dogaro da daidaituwa, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, al'ada da kuma muhalli.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter salo ne na kawar da hankalin 'yan kasa daga gazawar FG, Ortom

Sunayen biranen duniya mafi muni a 2021 ya bayyana, Legas ce ta biyu
Sunayen biranen duniya mafi muni a 2021 ya bayyana, Legas ce ta biyu. Hoto daga Olukayode Jaiyeola, Riccardo Savi
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Mutumin da ya kwashe shekaru 50 yana tara motoci kasaitattu ya tara har 3000

Ga jerin sunayen birnane 10 mafi munin da za a iya rayuwa a duniya a 2021:

1. Damascus, Syria (140)

2. Lagos, Nigeria (139)

3. Port Moresby, PNG (138)

4. Dhaka, Bangladesh (137)

5. Algiers, Algeria (136)

6. Tripoli, Libya (135)

7. Karachi, Pakistan (134)

8. Harare, Zimbabwe (133)

9. Douala, Cameroon (132)

10. Caracas, Venezuela (131)

Kamar yadda Legit.ng ta gano, biranen da suk afi yawa a jerin duk a nahiyar Afrika suke.

A daya bangaren, birnin Auckland dake New Zealand ne ya zama birnin da yafi ko ina dadin zama a duniya a 2021. Birnin Osaka na kasar Japan ne na biyu, birnin Adelaide na Australia ne ya zama na uku.

Daya daga cikin abubuwan da yasa birnin Auckland ya zama na farko a wannan jerin, shine yadda suka yi kokarin dakile annobar korona.

Ga jerin sunayen birane masu dadin zama 10 a duniya a 2021:

1. Auckland, New Zealand

2. Osaka, Japan

3. Adelaide, Australia

4. Wellington, New Zealand

5. Tokyo, Japan

6. Perth, Australia

7. Zurich, Switzerland

8. Geneva, Switzerland

9. Melbourne, Australia

10. Brisbane, Australia

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce kamfanin Twitter, ya garzaya domin neman sasanci da gwamnatin Najeriya.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar ta tarayya.

Ya bayyana cewa tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu saboda an samu rahotanni na gagarumar asarar da twitter ta dinga tafkawa na biliyoyi, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel