Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke 'Yan bindiga da bokan da suka kona gidan Gwamnan Imo

Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke 'Yan bindiga da bokan da suka kona gidan Gwamnan Imo

• ‘Yan Sanda sun kama wadanda ake zargi da kai hari gidan Gwamna Hope Uzodinma

• Wadannan ‘Yan bindiga ne suka rika kona ofisoshin ‘Yan Sanda kwanaki a jihar Imo

• Jami’an sun kama wani tsoho wanda ya taimaka wajen cafke sauran ‘Yan ta’addan

A ranar Alhamis, rundunar ‘yan sanda na jihar Imo, ta bada sanarwar damke wadanda ake zargi sun kai hari a gidan dangin Gwamna Hope Uzodimma.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa mutane tara suka fada hannun jami’an ‘yan sanda a halin yanzu, kuma sun amsa laifuffukan da ake zarginsu da su.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya fitar da rahoto, daga cikin wadanda aka kama har da wani mai maganin gargajiya da ke ba mutane surkulle.

KU KARANTA: Mun kama mai ba 'Yan IPOB asiri - 'Yan Sanda

Wannan mai magani shi ne yake taimaka wa ‘yan ta’addan kungiyar IPOB Eastern Security Network (ESN) da magunguna domin su kai hare-hare.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sanda na jihar Imo, Bala Elkana, a madadin kwamishinan ‘yan sanda.

A jawabinsa, SP Bala Elkana ya ce:

“A ranar 8 ga watan Yuni, 2021, da kimanin karfe 4:30 na yamma, dakarun musamman bayan sun samu bayanan sirri su la dura Ukwuorji, a karamar hukumar Mbaitoli da kuma hanyar Onitsha, suka cafke wani namiji, EZEUGO ORDU mai shekara 65, ‘dan garin Ubachima, Omuma, karamar hukumar Oru ta yamma.”

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari a Benuwai, sun kashe mutane

Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke 'Yan bindiga da bokan da suka kona gidan Gwamnan Imo
Motar ‘Yan Sanda Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Ya amsa cewa ya na cikin ‘yan kungiyar IPOB/ESN, ya kuma yi bayanan da suka taimaka wa ‘yan sanda a kan hare-haren da aka kai wa ofisoshin ‘yan sanda da gidan gwamna Hope Uzodinma.”

Elkana ya ce wannan mutum ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wani jeji a kusa da rafin Njaba inda sojojin IPOB/ESN suke boye, su ka cafke mutum tara yayin da suke shirin kai wani harin.

Bayan haka jami'an tsaron sun karbe wasu kayan surkule da makamai da ke hannunsu.

Jami'in ya ce wani CHINEDU NWAKAIRE da UZOAMAKA UGOANYANWU ake zargin sun kai wa gidan gwamna da ofishin ‘yansanda hari, sun kuma amsa laifinsu da kansu.

Dazu kun ji cewa hukumar EFCC ta damke wani Matashi da yake hada mutane da ‘Yan damfara a Legas. Har da mahaifin wannan yaro yanzu ya shiga hannun hukuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel