Gwamnatin Najeriya ta zabi Litinin a matsayin ranar hutu, saboda murnar dawowar damokaradiyya

Gwamnatin Najeriya ta zabi Litinin a matsayin ranar hutu, saboda murnar dawowar damokaradiyya

- Rauf Aregbesola ya ce babu aiki a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, 2021

- An zabi wannan rana domin bikin tunawa da dawowar mulkin farar fula

- Ministan ya yi kira ga mutane su guji biyewa masu kiran a raba Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin, 14 ga watan Yuni, 2021, a matsayin ranar hutu domin ayi bikin murnar dawowar mulkin farar hula a Najeriya.

Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin Mai girma Ministan harkokin cikin gida na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranar Alhamis, a madadin gwamnati.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya taya mutanen Najeriya zagayowar wannan muhimmiyar rana, ya na mai kira ga al’umma su ba gwamnati mai-ci goyon-baya.

KU KARANTA: Buhari ya gargadi matasa su shiga taitayinsu

Ma’aikatar harkokin cikin gida na tarayya ta fitar da wannan sanarwa ta shafin Facebook a dazu ta bakin sakataren din-din-din na kasa, Dr. Shuaib Belgore.

A jawabinsa, Rauf Aregbesola, ya yi kira ga mutane su yi watsi da duk wani kira na raba Najeriya, ya ce abin da ya fi dacewa shi ne kasar ta zauna a dinke.

Ministan ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su rungumi hadin-kai da zaman lafiya domin a samu cigaba, Aregbesola ya ce akwai alamun za a kai ga ci wata rana.

Tsohon gwamnan na jihar Osun ya ce jama’a su tuna da saida ran da shugabannin baya su ka yi.

KU KARANTA: Aiki a tsarin farar hula akwai wahala - Buhari

Gwamnatin Najeriya ta zabi Litinin a matsayin ranar hutu, saboda murnar dawowar damokaradiyya
Shugaba Buhari Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Ga abin da jawabin yake cewa:

“Yayin da mu ke ganin zuwan wata ranar tunawa da damokaradiyya a kasarmu, muyi tuntuntuni a kan kokarin da shugabannin farko suka yi na ganin Najeriya ta tsaya a dunkule. Babu wani cigaba da za a iya samu idan ana rike da kulli a rai.”

Rauf Aregbesola ya kara da cewa: Da kalubalen da muke fuskanta yau a Najeriya, ina ganin damar kara dunkulewa, mu fadawa kanmu gaskiya, mu godewa juna, mu fahimci juna, mu karrama juna, mu zauna tare cikin zaman lafiya da aminci.”

Dazu kun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sha yabo bayan ya ƙaddamar da layin dogon Legas zuwa Ibadan da aka kashewa fiye da N600bn.

Tashar jirgin kasa ta Mobolaji Johnson itace tashar jirgin kasa mafi girma yanzu a yankin nahiyar Afirka ta Yamma wacce ke iya daukar fasinjoji 6,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel