Haramta Twitter: Kungiyar NBA ta tanadi zakakuran Lauyoyi 13 da za su gwabza da Gwamnati a kotu
- Kungiyar NBA ba ta amince da matakin dakatar da amfani da Twitter ba
- Lauyoyin kasar nan za su kai karar Gwamnatin Tarayya zuwa gaban kotu
- Isa Pantami da Lai Mohammed za su wakilci Gwamnati a zauna da Twitter
Kungiyar lauyoyi ta kasa ta shirya zuwa kotu da gwamnatin tarayya kan matakin da ta dauka na dakatar da amfani da kafar sada zumunta na Twitter.
Sakataren yada labarai na kungiyar NBA ta kasa, Dr. Rapulu Nduka, ya yi hira da Punch ta wayar salula, ya tabbatar da shirinsu na kai gwamnati kotu.
Da yake magana a ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2021, Rapulu Nduka, ya ce sun kafa wani kwamiti mai dauke da mutum 13 da zai duba lamarin.
KU KARANTA: Gwamnati za ta bi ta kan Whatsapp, Instagram, da Facebook
Wannan kwamiti ne zai yi aikin shigar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zuwa gaban Alkali. Vanguard ta ce NBA ta na ja da gwamnatin kasar.
Tun tuni kungiyar NBA ta ce za ta shigar da kara. Nduka yake cewa abin da ya hana su zuwa kotu kafin yanzu shi ne dogon yajin aikin ma’aikatan shari’a.
“Daga cikin aikin kwamitin shi ne ya dauki matakin da ya dace wajen kawo karshen matsalolin da mu ke ciki, musamman wuce gona da irin masu mulki.”
"Dr. Charles Mekwunye, zai jagoranci kwamitin tare da Dr. Olumide Ayeni (SAN). Sauran ‘yan kwamitin sune; Dr. Paul Ananaba (SAN), da Kunle Edun."
KU KARANTA: Ana ganin amfanin hana Twitter - APC
"Sai kuma Aderemi Oguntoye, Boonyameen Lawal, Solomon Oho, Gloria Ballason, Malachy Odo, Olumide Babalola, Baba Isah, Amaka Ezeno, da Auwal Yau."
A daidai wannan lokaci ne aka ji cewa Ministocin labarai da na tattalin arzikin zamani da sadarwa, Lai Mohammed da Isa Pantami za su gana da Twitter.
Ministocin za su jagoranci bangaren gwamnatin Najeriya a zaman da za su yi da kamfanin domin ganin yadda duka bangarorin za su samu mafita mai bullewa.
A yau ne aka ji cewa neman goge manhajar Twitter ya fallasa sirrin Abubakar Malami a idanun Duniya, inda aka gano ya na amfani da manhajar Cryptocurrency.
Haka zalika duk da an haramta aiki da manhajojin VPN, ana zargin Ministan shari'ar kasar ya yi amfani da manhajar domin ya hau Twitter akalla a karon karshe.
Asali: Legit.ng