Kotu ta yanke hukuncin dauri a kan wanda ya mari Shugaban Faransa a bainar jama’a

Kotu ta yanke hukuncin dauri a kan wanda ya mari Shugaban Faransa a bainar jama’a

  • Kotu ta zartar da hukuncin daurin watanni 18 kan Damien Tarel a garin Valence
  • Damien Tarel zai shafe watanni hudu a gidan kaso saboda marin shugaban kasa
  • Amma idan har matashin ya taki sa’a, ba dole ba ne a tsare shi a gidan kurkuku

Channels TV ta ce wata kotu a kasar Faransa ta yanke hukuncin dauri a gidan yari ga mutumin da aka kama da laifin marin Shugaban kasa Emmanuel Macron.

A ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, 2021, Alkali ya zartar da hukuncin daurin watanni 18 a kan Mista Damien Tarel a dalilin sharbawa shugaban Faransa mari

Damien Tarel mai shekara 28 da haihuwa ya na daure tun bayan da ya mari Emmanuel Macron yayin da ya fito rangadi a kudancin kasar Faransa a ranar Talata.

KU KARANTA: An sharara wa Shugaban Faransa Emmanuel Macron mari

Tarel zai shafe watanni hudu ne kacal a gidan maza domin an dakatar da ragowar watannin 14.

Kamar yadda jaridar J Post ta rahoto dazu, Lauyan da ya kai karar wannan mutum, Alex Perrin, ya ce abin da ya yi bai dace ba, ya ce ya takali rigima da gangan.

Alex Perrin ya yi magana da ‘yan jarida a gaban kotun garin Valence, bayan ya shigar da kara.

A dokar kasar Faransa, za a iya yin rangwame a duk wani hukuncin dauri a gidan yarin da bai kai shekaru biyu, ta yadda za a tsare mai laifin a wajen kurkuku.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron

Kotu ta yanke hukuncin dauri a kan wanda ya mari Shugaban Faransa a bainar jama’a
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Hoto: www.politico.eu
Asali: UGC

Akwai yiwuwar ba za a garkame Tarel a gidan yari ba, duk da wannan mutumi ya aikata babban laifi.

Da yake magana da gidan talabijin BFM, Tarel ya ce abubuwa suna tabarbarewa a kasar Faransa a karkashin jagorancin shugaba Macron, don haka ya mare shi.

Duniya ta yi wa wannan mutashi zafi, ya kammala karatu bai da aikin yi, kuma ya na zama da budurwarsa mai larura, sai ya huce takaicinsa da ya hadu da Macron.

A makon nan kun ji labarin wasu 'yan Najeriya da suka shiga littatafan tarihi a Turai, su ka lashe zabukan zaba Kansila a Amurka da kujerar jami'a a kasar Scotland.

Sunan Aisha Akinola ya samu shiga a Jami’ar Edinburgh mai dadadden tarihi yayin da Steve Ezeonu ya lashe kujerar kansilan gundumar Grand Pierre a Texas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel