Intabiyu da Buhari: Muhimman abubuwa 5 da shugaban kasa ya fada

Intabiyu da Buhari: Muhimman abubuwa 5 da shugaban kasa ya fada

- Bayan lokaci mai tsawo, Buhari yayi hira da manema labarai

- Bai kamata ku ci gaba da zura mini ido in magance muku dukkan matsalolinku ba, Buhari ga Gwamnoni

- Ko sun cire kansu daga kasar, ba su da wata makoma,” inji Buhari kan IPOB

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana matsayarsa game da wasu batutuwan da ke faruwa a Najeriya.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya fada a yayin wata tattaunawa da kafar telebijin ta Arise ta watsa:

1. "Idan kuka bari yunwa ta addabe mu, to gwamnati za ta shiga cikin matsala kuma ba ma son shiga matsalar. Matsalolin sun riga sun kai mana iya wuya."

2. "Ya kamata a samu wadannan mukaman. Akwai mutanen da suka shafe shekara 10 zuwa 15 a kan mukaman nan."

3. "Kungiyar ’yan aware ta IPOB ba wata aba bace, tana nan tamkar da digo a cikin da’ira. Ko da suna son ballewa, ba su da inda za su nufa."

4. "Kun fi ni sanin mutanen, sannan an zabe ku ta hanyar dimokoradiyya domin kare al’ummominku. Ba wai za ku zauna ku mike kafa ku yi tsammanin ni zan muku komi, ku dauki mataki."

5. "Akwai Barebari da Hausawa da Fulani a Jamhuriyar Nijar haka nan ma akwai Yarbawa a Benin. Ba zai yiwu haka kawai ka cire daga ’yan uwansu ba."

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Intabiyu da Buhari: Muhimman abubuwa 5 da ya shugaban kasa ya fada
Intabiyu da Buhari: Muhimman abubuwa 5 da ya shugaban kasa ya fada Hoto: Arise News
Asali: Facebook

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Hakazalika, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga karagar mulki, gonarsa zai koma domin kula da shanunsa.

“Ban taba barin gonata ba. Har yanzu ina da shanu masu yawa. Zan ci gaba da zuwa gona kullum domin samun abin da zai debe mini kewa,” kamar yadda ya fada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel