Bidiyon mahaifin amarya yana kwasar rawa a liyafa, baki sun matukar shan mamaki
- Mahaifin wata amarya ya kayatar da wurin shagalin bikin diyarsa bayan ya shiga filin rawa domin nishadantar da baki
- Mutumin yayi rawa mai kyau da ban sha'awa kuma kowa ya sha mamaki da yanayin da yake rausaya baki suna ihu da sowa
- A bidiyon da wani ya wallafa na biki a kafar sada zumuntar zamain, mahaifin amaryar ya sha tsokaci masu tarin yawa
Wani bidiyo mai matukar kayatarwa ya bayyana a kafar sada zumunta inda aka ga mahaifin amarya yana nuna kwarewarsa a rawa wurin bikin diyarsa.
A liyafar auren, mahaifin amaryar ya shiga wurin rawa da tsarinsa wanda yasa dukkan baki suka dinga tafi da sowa.
KU KARANTA: Birane 5 dake karkashin kasa, wurin da suke da labaransu masu cike da al'ajabi
KU KARANTA: Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna
A bidiyon da wani @official_mcbobo ya wallafa a Instagram, mahaifin amarya, ango da abokan ango sun cashe iyakar iyawarsu.
Angon da abokansa sun dinga bin mahaifin amarya daki-daki wurin rawan yayin da baki suka dinga ihu da tafi.
Ga jerin tsokacin da jama'a suka dinga yi kan bidiyon:
@beecrownevents yace: "Mahaifin amaryan nan ne ya kawo karshen wannan liyafar... Na jinjina maka Mc Bobo."
@teetohkiddieshub kuwa cewa yayi: "Liyafa ta kusa tashi. Mahaifin amarya 'dan gari' ne."
@wal_pops yace: "Ban so kawo karshen bidiyon nan ba."
Jama'a da dama suna da hanyoyin nuna farin cikinsu idan abun murna ya samesu, hakan ne yasa zaka ga suna rawa wurin liyafa ko kuma dai wani abu mai bayyana farin ciki karara.
A wani labari na daban, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce nan babu dadewa za a shawo kan matsalar rashin tsaro kuma Najeriya zata samu zaman lafiya.
Ministan wanda ya samu wakilcin Lucky Irabor, shugaban ma'aikatan tsaro, ya sanar da hakan ne a wani taro kashi na 57 da aka yi a NAF Makurdi, babban birnin jihar Binuwai.
Ana samun jerin hare-hare a fadin kasar nan wanda ke kawo mutuwar jama'a, garkuwa da mutane da kuma kona gine-ginen gwamnati, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng