Uba da ‘Dan cikin da ya haifa sun fada hannun EFCC bisa zarginsu da laifin ‘Yahoo-Yahoo’

Uba da ‘Dan cikin da ya haifa sun fada hannun EFCC bisa zarginsu da laifin ‘Yahoo-Yahoo’

- ‘Yan Sanda sun kama wani mai suna Malik Bakare, sun mika shi ga EFCC

- Jami’an EFCC suna zargin wannan matashi ya na taimakawa ‘Yan damfara

- Mahaifin Malik Bakare ya fada wa tarkon EFCC bayan ya je karbar motarsa

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta soma bincike a kan zargin da ake yi wa wani Malik Bakare na laifin yin karya da satar dukiyar mutane ta yanar gizo.

EFCC mai binciken masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta bada wannan sanarwa a shafinta na Facebook ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2021.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, ofishin hukumar da ke garin Legas ne yake wannan bincike.

KU KARANTA: Shugaban EFCC, Bawa ya fadi abin da zai iya sa ya ajiye aiki

Taken da hukumar ta yi wa sanarwar shi ne: ‘Son, Father in EFCC’s Net for Alleged Internet Fraud’, amma ta ce sai nan gaba za a fitar da cikakken rahoto.

Jaridar Punch ta bi diddikin wannan bincike, inda ta gano cewa jami’an CID na ‘yan sanda suka cafke Malik Bakare, su ka mika wa hukumar EFCC shi.

‘Yan Sanda sun yi ram da wannan mutumi ne a yankin Alagbon, jihar Legas, a ranar 31 ga watan Mayu, 2021. Tun a wancan lokaci aka tsare shi, ana bincike.

“Binciken ya nuna cewa ya zama dillali, ya na hada mutane da masu damfara ta yanar gizo, sai ya karbi kasonsa da zarar an yi nasarar sacewa mutum kudi.”

KU KARANTA: EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Uba da ‘Dan cikin da ya haifa sun fada hannun EFCC bisa zarginsu da laifin ‘Yahoo-Yahoo’
Maik da Isa Bakare Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

Har ila yau an cafke mahaifin wannan matashi da ake zargi, a lokacin da ya zo ya na ikirarin shi ne ya mallaki wata mota kirar Range Rover SUV da aka karbe.

Jami’an EFCC sun karbi wannan mota ne daga hannun Malik Bakare. Mahaifinsa, Isa Bakare ya yi da’awar shi ya mallaki motar ba tare da nuna wata hujja ba.

Farashin wannan mota ya kai Naira miliyan 45, amma da aka tatse mahaifin yaron a gaba, bai iya bada bayani mai gamsarwa a kan yadda ya mallaki motar ba.

A jiya kun jii cewa ana zargin wani mutumi tsofai-tsofai da cinye kudin magada, magana ta kai gaban EFCC, kuma ana tuhumarsa da laifin wawurar N77m.

Har ila yau kun ji yadda hukumar EFCC ta yi ram da wani mutum da aka turawa kudi zai kawo mota, ya yi gaba da kudin wani Bawan Allah da ya kusa kai N25m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng