Mutumin da ya kwashe shekaru 50 yana tara motoci kasaitattu ya tara har 3000
- Son da Hamad yake wa motoci a bayyane yake duba da yadda ya tara har guda 3000 na kasaitattun motoci
- Wasu daga cikin motocin dake garejin mutumin dan asalin Abu Dhabi suna da dakunan bacci 3, wata kuma na iyo a ruwa
- Bayan shekaru 50 da yayi yana tara motocin, balaraben yace ya adana motocin a wata irin ma'adana mai siffar dala
Jama'a kala-kala ne, wasu na matukar kaunar kayan kyale-kyale, wasu wasanni suka fi so ko kuma girke-girke, amma ga Balarabe, motoci masu tsari da kyau yafi kauna.
Wani mutum balarabe mai suna Hamad ya mallaki motoci 3000 a garejinsa saboda tsabar kaunar motoci da yake yi.
KU KARANTA: Dakatar da Twitter salo ne na kawar da hankalin 'yan kasa daga gazawar FG, Ortom
KU KARANTA: Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari
A wani bidiyon YouTube da Nas Daily suka wallafa, mutumin dan asalin Abu Dhabi yace ya kwashe shekaru 50 yana tara motocin kuma ba gama-gari bane. Ya fi siyan motocin da basu da yawa a duniya.
Dukkansu yana adana su a garejinsa mai siffar dala. Wasu daga cikin kasaitattun motocin da ya mallaka sun hada da mai dakunan bacci uku, falo, mai siffar duniya, karama kalar gajimare, wacce ke iya yawo a saman ruwa, da sauransu.
Abun mamakin shine yadda babu Ferrari ko Lamborghini a cikin jerin motocinsa. Akwai yuwuwar tsohon sojan baya son motocin zamani.
Kamar yadda hamad yace, yana siya, gyarawa tare da mayar da motocin yadda yake so. Hamad yace haddadiyar mota ita ce duk wani abu da zai dauka mutum daga wannan wuri zuwa wani, ba dole ta zamani ba.
A wani labari na daban, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa za a yi sauye-sauye masu tarin yawa a bangaren yanayin tsaron kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya bada wannan tabbacin ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran gidan gwamnati bayan gabatar da sabon shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
An gabatar da shugaban rundunar sojin kasan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani taro da ya samu halartar shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor.
Asali: Legit.ng