Karya ta kare: Wasu ‘Yan kasuwa sun fada ragar Hukumar EFCC saboda zargin satar N102m

Karya ta kare: Wasu ‘Yan kasuwa sun fada ragar Hukumar EFCC saboda zargin satar N102m

- Hukumar EFCC ta ce ta kama wasu mutane biyu da laifin cin kudin Bayin Allah

- Jami’an hukumar da ke Legas sun cafke Emmanuel Obinyan da ya 'cinye' N77m

- Sannan an damke wani ya yi gaba da kudin wani mutumi da zai kawowa mota

Mun ji wani mutumi mai suna Emmanuel Obinyan ya shiga hannun hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

Jaridar nan ta Punch ta fitar da rahoto cewa EFCC ta cafke Emmanuel Obinyan ne bisa zargin yin karya da karkatar da wasu kudi har N77, 773, 700.

Kamar yadda muka samu labari a ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2021, wani Daniel Chinemelum, wanda yanzu ya rasu, ya taba yin hulda da Obinyan.

KU KARANTA: Mbaka ya cigaba da magana a kan siyasa duk da hana shi, DSS na nemansa

A shekarar 2015 ne Marigayi Daniel Chinemelum suka shiga yarjejeniya da wannan mutum da nufin za su kafa wani kamfani na kasuwancin gidaje.

Iyalen Marigayi Daniel Chinemelum da suka kai kara gaban hukuma, sun bayyana cewa mahaifinsu ya tura N52m a cikin asusun bankin Obinyan.

‘Ya ‘yan mamacin, Daniel, Stephen da kuma Emeka sun ce tsohonsu ya aika wa wannan mutumi wadannan kudi ne a matsayin kasonsa a kasuwanci.

Yaran suka ce a shekaru biyar da aka yi na wannan yarjejeniyar sun shude, Obinyan bai iya yi masu bayanin ribar da aka samu ko rashin da aka yi ba.

KU KARANTA: ‘Yan bindigan da suka sace Yaran Islamiyya sun ce a kawo N150m

Karya ta kare: Wasu ‘Yan kasuwa sun fada ragar Hukumar EFCC saboda zargin satar N102m
Emmanuel Obinyan da Rasaki Wasiu Adeyiga Hoto: www.facebook.com/officialefcc
Asali: Facebook

Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC na kasa, Wilson Uwujaren, ya ce bayan iyalan mamacin sun gagara karbo kudinsu, sai suka kawo kararsa.

EFCC a shafinta na Facebook ta tabbatar da cewa a dalilin haka ta cafke Mista Obinyan, tare da wani Rasaki Adeyiga, shi kuma bisa zargin satar N24, 260, 000.

Adeyiga ya gabatar da kan shi wajen wani Ahmed Shinkafi a matsayin dillalin motoci daga Amurka da Turai, ya karbi miliyoyin kudi zai sayo masa mota.

Daga baya Ahmed Shinkafi ya kai kara wajen EFCC, ya ce ya tura wa Adeyiga N25m domin ya sayo masa mota, amma sai ya bi wadannan kudi ya lamushe.

Dazu nan ku ka ji cewa babban Lauya mai kare hakkin jama'a, Mike Ozekhome SAN, ya ce Gwamnatin tarayya ba ta isa ta hana jama’a amfani da Twitter ba.

Mike Ozekhome ya ce sai dai ayi a gama, amma haramta Twitter a kasar nan ba zai yiwu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel