Gwamnatin Buhari ta yarda a batar da Naira Biliyan 770 wajen sayawa Sojoji kayan yaki

Gwamnatin Buhari ta yarda a batar da Naira Biliyan 770 wajen sayawa Sojoji kayan yaki

- FEC ta amince a aikawa Majalisar Najeriya sabon kasafin kudi na N895bn

- Ministar tattalin arziki ta bayyana amfanin da za ayi da wadannan kudi jiya

- Zainab Ahmed ta ce daga ciki ne za a saye makamai da rigakafin COVID-19

A ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2021, majalisar zartarwa ta tarayya watau FEC, ta amince da sabon kasafin kudin N895, 842,462,917 da aka shirya.

Gwamnatin tarayya ta sake fitar da wani kundin kasafin kudi domin ya cike gibin da aka samu a shekarar nan, inda za a yi amfani da kudin a harkar tsaro.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar FEC ta amince a batar da wadannan makudan kudin a wajen sayen makamai da kuma rigakafin cutar COVID-19.

KU KARANTA: Neman goge manhajar Twitter ya fallasa asirin Ministan shari'a

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattali, Zainab Ahmed, ta shaidawa manema labarai wannan bayan an tashi daga taron FEC da aka yi jiya a fadar Aso Villa.

Haka zalika Zainab Ahmed ta ce an ware N83.56b domin a sayo rigakafin cutar Coronavirus. A nan ne za a samu kudin fansar rigakafi miliyan daga ketare.

Bayan haka Ahmed ta ce akwai Naira biliyan 40 da aka tanada domin a biya ma’aikatan lafiya da malaman manyan makarantu wasu dinsu da su ke bin bashi.

Ministar ta ce akwai Naira biliyan 1.69 da aka sa domin shirin yaki da cutar kanjamau a Najeriya.

KU KARANTA: ‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da yara a Neja sun ce a kawo N150m

Gwamnatin Buhari ta yarda a batar da Naira Biliyan 770 wajen sayawa Sojoji kayan yaki
Ministar kudi, Zainab Ahmed Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

A cewar Ministar Naira biliyan 770 za su tafi ne wajen sayen makaman da jami’an tsaro suke bukata a yanzu. Daily Nigerian ta tabbatar da wannan rahoton ta.

“FEC ta amince a dumfari majalisar tarayya domin ta amince a kashe wadannan kudi.” Ahmed ta yi bayanin yadda za a samu wannan kudi da ya kusa kai Tiriliyan.

Gwamnatin tarayya za ta ci bashin Naira biliyan 722 domin ayi maganin matsalar tsaro. Ministar ta ce za a nemo aron kudin ne daga bankunan gida da na waje.

A jiya ne aka ji Karamin Ministan harkar mai a Najeriya, Timipre Sylva ya na cewa zancen da ake yi na cewa su na fada a kan rikon NDDC karyar banza da wofi ce.

Sylva ya ce sam babu rigimar da ta shiga tsakaninsa da Maigidansa, Sanata Godswill Akpabio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel