Mambilla: Gwamnati ta ware Biliyan 2.6 a matsayin gudumuwarta a 2020
Daily Trust ta yi wani dogon bincike game da sha’anin kwangilar wutar lantarkin da ke Garin Mambilla a jihar Taraba. Shekaru 40 kenan da bada kwangilar amma har yau shiru ake ji.
Jaridar ta bayyana cewa an fara bada kwangilar wannan aiki ne a 1973. A 2007 aka gwamnatin Obasanjo ta sake tado da maganar wanda shi kuma Marigayi Umaru Yar’adua ya soke kwangilar.
Bayan dogon daukar dogon lokaci, hukumar BPP ta kakakkabe takardun wannan aiki inda aka sa ran kamalla aikin a 2012. Bayan gama wannan shiri ne kwatsam sai aka maga gwamnati a kotu.
Bayan wannan rikici, gwamnatin Najeriya ta ci damar kammala aikin da zai samar da megawatt 3050 a shekarar 2015. Kamfanin EXIM na kasar Sin aka sa rai zai bada 75% na kudin kwangilar.
Kudin wannan aiki da kamfanin CGGC da Sinohydro Corporation za su yi ya karu a mulkin nan, daga Dala biliyan 3.2 zuwa Dala biliyan 5.972 wanda a kudin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 2.
A 2017 hukumar BPP ta ba ma’aikatar wuta sabon satifiket na samun damar fara wannan aiki da nufin cewa gwamnatin tarayya za ta nemo inda za a samu tiriliyoyin kudin da za a yi aikin.
KU KARANTA: Za a ba Najeriya wani bashi domin gyara wutar lantarki
Gwamnatin za ta bada 15% na kudin aikin ne yayin da kamfanonin da za su dauki nauyi za su bada kaso mafi tsoka. A kasafin kudin 2020, gwamnatin tarayya ta ware wasu kudi na aikin.
Shugaban kasa Buhari ya yi kasafin biliyan 2 da za su tafi wajen aikin wutar lantarki. Bugu da kari an ware miliyan 600 a matsayin abin da za a ba kwararrun da ke bincike a game da aikin.
Za a kashe miliyan 600 ne wajen duba Mazauna Garin na Mambilla da aikin zai shafa da tsare-tsare da duba aikin da kuma aikin da kwamitin gwamnatin tarayya da jihar Taraba za su yi.
Kauyuka 10000 za a tada idan aka fara wannan aiki. Za a ba kowa kudin sallama domin su nemi wani matsugunin. Binciken da aka yi ya nuna babu wasu ‘yan kwangila da su ka iso yankunan.
Idan aka kammala wannan aiki Najeriya za ta samu karin sama da megawatt 3000 na lantarki. Yanzu haka dai abin da tashar Shiroro Kainji da Jebba su ke badawa bai wuce megawatt 2000 ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng