Asirin Ministan Shugaba Buhari ya tonu wajen kokarin goge Twitter daga wayar salularsa

Asirin Ministan Shugaba Buhari ya tonu wajen kokarin goge Twitter daga wayar salularsa

- AGF ya na aiki da manhajar Cryptocurrency da VPN da aka hana a Najeriya

- An gano akwai manhajojin VPN da LATOKEN a wayar Abubakar Malami

- A 2017 aka kirkiri manhajar LATOKEN domin yin cinikin kudin yanar gizo

Rahotanni daga jaridar Premium Times sun ce a wajen neman kiba, Mai girma Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya ci karo da rama.

Yayin da Abubakar Malami ya ke kokarin nunawa Duniya cewa ya goge Twitter daga wayarsa, an kuma gano ya na aiki da wasu haramtattun manhajoji.

Hoto da bidiyo sun tabbatar da cewa a wayar salular Abubakar Malami SAN, akwai manhajar cryptocurrency wanda gwamnatinsa ta haramta aiki da shi.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter zai iya jefamu a matsala - 'Yan kasuwa

A baya CBN gwamnatin Muhammadu Buhari, wanda Malami ne babban lauyanta, ta bada umarnin hana duk wata irin mu’amala da kudin yanar gizo.

A ranar da Ministan ya ke nuna ya goge Twitter daga wayarsa, an ga tambarin wata manhaja da ake amfani da ita wajen cinikin irin wannan kudi na gizo.

Da ya wallafa hoton da taken “My Twitter Account Deactivated”, ita ma Punch ta yi binciken kwa-kwaf, ta gano akwai manhajar nan ta Latoken a wayar Ministan.

Tambarin ‘LA’ a sashen dama da ke saman wayar Ministan shari’ar ya tabbatar da wannan, za a gane cewa manhajar ta na neman Malami ya sa lambar wayarsa.

KU KARANTA: Twitter ta garzaya wurin Gwamnati, tana neman sulhu

Asirin Ministan Shugaba Buhari ya tonu wajen kokarin goge Twitter daga wayar salularsa
Abubakar Malami ya goge Twitter Hoto: www.kanyidaily.com
Asali: UGC

Mutane sun shiga shafukan sada zumunta suna ta surutu a kan lamarin, inda wasu suke ganin Ministan ya saba doka, wasu kuma suna cewa babu hujjar hakan.

Masu kare shi sun ce ana amfani da manhajojin wajen sayen katin wayar salula. Sai dai kuma an ga tambarin manhajar VPN wanda shi ma an haramta aiki da shi.

A gefen dama akwai tambarin haramtacciyar manhajar VPN wanda ake zargin da ita ne Ministan ya iya samun damar hawa Twitter domin ya goge shafin na sa.

Fitaccen Lauyan nan da ke kare hakkin Bil Adama a Najeriya, Cif Mike Ozekhome SAN, ya soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan amfani da Twitter.

Ozekhome SAN ya fadawa Ministan shari'a, Abubakar Malami cewa gidajen yari za su cika makil idan dai aka ce za a kama mutane saboda suna amfani da Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel