Jita-jita ta na yawo cewa Ministocin Buhari suna fada a kan rabon kujerun hukumar Neja-Delta

Jita-jita ta na yawo cewa Ministocin Buhari suna fada a kan rabon kujerun hukumar Neja-Delta

- Timipre Sylva ya fito ya musanya jita-jitar rikici tsakaninsa da Godswill Akpabio

- Wani Hadiminsa ya ce Maigidansa ya dauki Godswill Akpabio a matsayin ‘danuwa

- Sylva ya ce babu abin da ya hada shi da rigima a kan wadanda za su rike NDDC

Karamin Ministan harkokin Neja-Delta na kasa, Timipre Sylva, ya ce babu abin da ya shiga tsakaninsa da babban Minista, Sanata Godswill Akpabio.

Jaridar The Guardian ta fitar da rahoto a ranar Talata, 8 ga watan Yuni, 2021, inda aka ji Timipre Sylva ya karyata rade-radin samun jita-jita da maigidansa.

Hadimin Ministan, Julius Bokoru, ya yi magana a madadinsa, ya na cewa masu kirkira da yada labarin rashin fahimta tsakaninsu, ‘yan hana ruwa gudu ne.

KU KARANTA: Ministan shari'a bai isa ya hana jama’a amfani da Twitter ba - Lauya

A jawabin da ya fitar, mai taimakawa Ministan wajen yada labarai ya yi kira ga mutane su yi watsi da wannan jita-jita da suke yawo, ya ce ba su da wani tushe.

The Nation ta rahoto karamin Ministan harkan man ya na musanya zargin da ake yi masa na kokarin hana wadansu zama shugabanni a hukumar NDDC.

“Wannan labari ba gaskiya ba ne, ba komai ba ne face wasu tarkacen karyayyaki da aka kitsa, wanda ya kamata kowa ya yi fatali da su.” Inji Mista Bokoru.

“Sylva da Akpabio sun dade suna da kyakyyawar alaka, suna ganin junansu a matsayin ‘yanuwa, masu gwagwarmaya wajen kawo wa Neja-Delta da kasa cigaba.”

Bokoru ya kara da cewa: "A yanzu Sylva ya na karbar masaukin baki a taron Nigeria International Petroleum Summit, bai tunanin wadanda zasu rike NDDC."

Jita-jita ta na yawo cewa Ministocin Buhari suna fada a kan rabon kujerun hukumar Neja-Delta
Timipre Sylva da wasu manyan kasa Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC ta kama 'Yan kasuwa da ake zargi da laifin satar N102m

“Sai dai ma ya na addu’ar cigaban yankin, a samu kwararru, masu kishi, da tausayi da kokarin aiki da za su shiga cikin majalisar da ke sa ido a kan aikin NDDC.”

An kitsa labarin ne da nufin kawo matsaloli da hatsaniya a Neja-Delta. Ya ce: “Ana kira ga mutane su yi watsi da rahoton, karya ne, sharri ne, neman cin mutunci ne.”

A safiyar yau ne aka ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed ya fatattaki dukkanin Kwamishinoni da kusan duka daga cikin Hadimansa.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Zamfara ya dauki irin wannan mataki. An dade ana rade-radin gwamna Bello Matawalle ya na shirin barin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel