Gidajen yari za su cika makil idan aka ce za a kama mutane saboda Twitter inji Ozekhome SAN

Gidajen yari za su cika makil idan aka ce za a kama mutane saboda Twitter inji Ozekhome SAN

- Mike Ozekhome ya yi wa AGF raddi a kan umarnin cafke masu amfani da Twitter

- Lauyan ya bayyana cewa sai an tanadi wasu gidajen yarin idan za a kama mutane

- Ozekhome SAN ya ce ina ma gwamnati ta na wannan gaggawa wajen kawo tsaro

Lauyan nan mai kare hakkin Bil Adama a Najeriya, Cif Mike Ozekhome SAN, ya soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan amfani da Twitter.

Jaridar Vanguard ta rahoto Mike Ozekhome SAN ya na cewa gwamnatin tarayya ta shirya gina dubunnan gidajen yari da za ta daure masu saba dokarta.

Lauyan ya ce za a samu mutane da yawa wanda zai yi wahala su bi dokar da gwamnati ta kakaba.

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun cigaba da amfani da dandalin Twitter

Da yake magana, Mike Ozekhome ya yi tir da yadda gwamnatin kasar ta yi garajen haramta amfani da Twitter, ba tare da ta yi la’akari da fuskar tattalin arziki ba.

Babban lauyan ya aikawa ‘yan jarida takarda, ya ce hana Twitter ya na cikin dabarar Muhammadu Buhari na cafke ‘yan adawa da kuma ‘yan gwagwarmaya.

A farkon makon nan, Punch ta rahoto Lauyan ya na cewa:

“Babban lauyan gwamnatin tarayya, Ministan shari’a, Abubakar Makami SAN, ya bada umarni ayi maza a soma gurfanar da wadanda suka saba dokar hana Twitter a Najeriya. Ya na so DPP ta hada-kai da ma’aikatar sadarwa, da NCC da sauran hukumomi su fara gurfanar da mutane ba tare da wata-wata ba.”

KU KARANTA: Gwamnati ta fito da sunayen matasan da za su iya samun aikin N-Power

Gidajen yari za su cika taf idan aka ce za a kama mutane saboda Twitter - Ozekhome
Cif Mike Ozekhome SAN Hoto: www.mikeozekhomeschambers.com
Asali: Facebook

“Ina ma ace gwamnatin APC ta su Malami ta nuna irin wannan gaggawa wajen matsalar rashin tsaro da ke damun kasa, da harkar tattalin arziki da rashin gaskiya da su ka yi mana katutu.”

“Malami ya yi wannan ne tare da Lai Mohammed, saboda suna da masaniya cewa mutanen Najeriya sun soma amfani da manhajojin VPN domin su kaurcewa takunkumin da aka sa.”

Jawabin Ozekhome ya cigaba da cewa: “Dole gwamnati ta shirya gina dubunnan gidajen yari a fadin lungu da sakokin Najeriya domin su daure ‘Yan Najeriya da za su saba dokar.”

A ranar Talata ne jam’iyyar APC ta fito ta na fadakar da ‘yan Najeriya game da hadurran da ke tattare da hawa shafin sada zumunta na Twitter ta hanyar amfani da VPN.

Sakataren kwamitin kula na rikon kwarya na jam'iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe ya ce za a iya satar bayanai ko kudin mutum daga asusun banki ta kafar VPN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel