Donald Trump ya jinjinawa Buhari kan dakatad da Tuwita a Najeriya

Donald Trump ya jinjinawa Buhari kan dakatad da Tuwita a Najeriya

-Tsohon shugaban kasan Amurka Donald Trump ya taya Nigeria farin cikin dakatar da shafin sada zumunta na twiter.

-Lai muhammad,minister yada labarai na kasa ne ya sanar da dakatarwan.

-A wata sanarwa data fito a ranar talata "Donald Trump ya bayyana farin cikinsa kuma yayi kira ga sauran kasashe da suyi koyi da hakan"

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya "taya" Najeriya murna game da dakatar da ayyukan Twitter a kasar.

A ranar 4 ga Yuni, Lai Mohammed, ministan labarai, ya ba da sanarwar dakatarwa mara "iyaka" na Twitter a Najeriya saboda ba da damar amfani da dandalinsu wurin ayyukan da "ke barazana ga zaman lafiyar Najeriya".

Sanarwar gwamnatin tarayya ya zo ne kwanaki kadan bayan da Twitter ta goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Donald Trump ya jinjinawa Buhari kan dakatad da Tuwita a Najeriya
Donald Trump ya jinjinawa Buhari kan dakatad da Tuwita a Najeriya Hoto: Presidency
Asali: Getty Images

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

A wata sanarwa a ranar Talata, Trump ya taya gwamnatin tarayya murna kan hukuncin, sannan ya bukaci sauran kasashe da su yi koyi da hakan.

“Ina taya kasar Najeriya murna, wanda suka dakatar da Twitter saboda sun dakatar da shugabansu. Ya kamata a samu karin kasashe da suka dakatar da Twitter da Facebook saboda rashin ba da yancin yin magana a bayyane - ya kamata a ji kowace murya,” in ji sanarwar.

A bangare guda, Gwamnatin Amurka ta yi kira da a gaggauta janye dakatar da aiki da Tuwita a Najeriya.

Kiran da Amurkar ta yi a yanzu, shi ne tsokaci da ta yi karo na hudu a cikin mako guda bayan dakatar da ayyukan Tuwita a Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta yi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Mai kula da Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka (USAID), Samantha Power, ta ce dakatarwar ba komai ba ce illa hana ’yancin fadin albarkacin baki da gwamnati ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng