'Dan Najeriya ya ci zabe a Amurka da kuri'a 180, ya doke ‘Dan kasa, Bayarabiya ta yi abin alfahari

'Dan Najeriya ya ci zabe a Amurka da kuri'a 180, ya doke ‘Dan kasa, Bayarabiya ta yi abin alfahari

- Steve Ezeonu ya yi nasara a zaben cike gurbin Kansila da aka yi a Texas, Amurka

- ‘Dan Najeriyar da ya tsaya takara a jam’iyyar Democrat ya doke Mr. Greg Giessne

- A kasar Scotland kuma, wata mutumiyar Afrika ce ta ci kujerar 'Sabatical Officer'

Punch ta fitar da rahoto cewa wani matashin Najeriya mai shekara 22 a Duniya, Steve Ezeonu, ya yi nasara a zaben cike gurbin zama kansila a kasar Amurka.

Steve Ezeonu ya lashe kujerar kansilan gundumar Grand Pierre a birnin Texas. Shugabar hukumar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta taya Ezeonu murna.

Jaridar Gazette ta ce NiDCOM ta aiko jawabin barka ne ta hannun shugaban yada labarai da hulda da jama’an hukumar, Abdur-Rahman Balogun a ranar Litinin.

KU KARANTA: Wani mutum ya shararawa Shugaban kasar Faransa mari

Mista Ezeonu wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar Democrat ya samu kuri’u 3, 908, inda abokin adawarsa, Mr. Greg Giessne, ya tashi da kuri’u 3, 720.

Jawabin ya ce ratar kuri’a 183 ta raba ‘yan takarar, Ezeonu ya samu 51.2%, yayin da Giessner ya iya lashe 48.8% na kuri’un da aka kada a zaben 5 ga watan Yuni.

A daidai wannan lokaci Nigerian Watch ta ce an samu wata budurwa haihuwar jihar Sokoto a Najeriya, da ta samu kujera a jami’ar Edinburgh da ke Scotland.

Aisha Akinola ta yi nasarar samun kujerar wakiliyar dalibai ta wannan jami’ar ta kasar Scotland.

'Dan Najeriya ya ci zabe a Amurka da kuri'a 180, ya doke ‘Dan kasa, Bayarabiya ta yi abin alfahari
Steve Ezeonu da Aisha Akinola Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan adawa suna so a tursasawa Gwamnati ta cire hanin Twitter

Jaridar Punch ta ce yanzu haka Aisha Akinola ce mataimakiyar shugaban da ke kula da jin dadin walwala na kungiyar daliban jami’ar Edinburgh mai tsohon tarihi.

Kamar yadda ta shaida wa ‘yan jaridar, ta ce ita kadai ce bakar fata da ta nemi wannan kujera, ta yi tunanin ba za ta ci ba, amma mahaifiyarta ta bata kwarin-gwiwa.

A cikin shekara 438 da kafuwar wannan jami’a, Akinola ce mutumiyar Afrikar farko da ta samu wannan dama. Ta ce tun da ta zo Scotland, ta kwallafa rai a kujerar.

A baya-bayan nan kun ji cewa Dr. Uzoma Emenike ta zama macen farko da aka nada Jakadar Najeriya zuwa kasar Amurka. Kujerar da babu macen da ta taba hawa.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi abin a yaba da ta zabi Uzoma Emenike ta zama wakiliyarta a kasar Amurka, bayan ta rike Ambasadar kasasshen Iceland da Ireland.

Asali: Legit.ng

Online view pixel