Haramta Twitter: ‘Yan Majalisar PDP sun yi fushi, sun fice daga zauren Majalisa a fusace

Haramta Twitter: ‘Yan Majalisar PDP sun yi fushi, sun fice daga zauren Majalisa a fusace

- ‘Yan Majalisar Tarayya sun yi muhawara a kan hana kamfanin Twitter aiki

- Shugaban Majalisa ya ba kwamitoci kwanaki su binciki matakin hana Twitter

- Masu hamayya sun bukaci Majalisa ta nemi Gwamnati ta janye dakatarwar

Wasu daga cikin ‘ya ‘yan PDP a majalisar wakilan tarayya a Najeriya sun nuna fushinsu a zaman da aka yi a yau Talata, 8 ga watan Yuni, 2021.

Jaridar Punch ta ce an samu wasu ‘yan majalisar hamayya da su ka fita daga zauren majalisa bayan Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ki sauraronsu.

‘Yan adawar suna zargin shugaban majalisar wakilan tarayya, da kin sauraron batun da suka kawo. The Guardian ta ce hakan ya kawo surutu.

KU KARANTA: Majalisa ta gayyaci Minista ya yi bayanin abin da ya sa aka dakatar da Twitter

Kamar yadda mu ka samu labari, ‘yan majalisar jam’iyyar adawa sun nemi a bukaci gwamnatin tarayya ta janye dakatarwar da aka yi wa Twitter.

A karshe Femi Gbajabiamila bai yi na’am da wannan a cikin matsayar da majalisar tarayyar ta dauka ba, ya ba kwamitoci umarni su yi bincike.

Shugaban majalisar wakilai na kasa, Gbajabiamila ya fadawa kwamitocin da abin ya shafa su gudanar da bincike, su gabatar da rahoto a kwana goma.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya ce idan aka tafi a haka, za a bar mutanen Najeriya su yi kwanaki ba su iya amfani da Twitter.

KU KARANTA: Gwamnoni su gama shiga jam’iyyar APC, nan gaba za a kama su - Ortom

Haramta Twitter: ‘Yan Majalisar PDP sun yi fushi, sun fice daga zauren Majalisa a fusace
Shugaban Majalisar Wakilai Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Honarabul Chinda ya na ganin a cikin wadannan kwanaki goma, an tauye hakkin jama’a, don haka ya bukaci a janye dakatarwar kafin a gama bincike.

Amma sai Rt. Hon. Gbajabiamila, ya kafa hujja da wata dokar majalisa da ta ce bai hallata a koma wa batun da aka kammala muhawara a kan ta a zaure ba.

Wannan uzuri da shugaban majalisar ya kawo bai yi wa ‘yan adawa dadi ba, hakan ya sa wasu da yawa daga cikinsu suka fita da sunan an hana su magana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng