Shekara 73 bayan barinsa gida, dattijo da aka yi tunanin ya dade da rasuwa ya bayyana a kauyensa a Kano

Shekara 73 bayan barinsa gida, dattijo da aka yi tunanin ya dade da rasuwa ya bayyana a kauyensa a Kano

- Wani dan Najeriya mai suna Olumuyiwa Adepitan ya taimaka wa wani dattijo koma wa kauyensa shekara 73 tafiyarsa zuwa Kudu maso Yamma

– Dattijon ya bar Kano domin ci rani kuma bai koma gida ba sai kwanan nan; ya yi sana’ar sayar da goro a Jihar Ondo

- Dan shekara 95 din wanda koma sana’ar noma ba shi da mata ko ’ya’ya

Wani dattijo dan shekara 95 mai suna Saidu Abdullahi, wanda ya bar gidansu a Kano a lokacin yana dan saurayi mai shekara 20 da ’yan kai da mutane da dama suka yi imanin cewa ya rasu, ya sake bayyana a Jihar Kanon.

Wani da ake kira Olumuyiwa Adepitan shi ne ya mayar da dattijon garinsa bayan ya share shekaru masu yawa a Jihar Oyo, rahoton TheCable.

Mutumin ya ce ya fice daga garin nasa inda ya nufi Ibadan a lokacin yana shekara 22 zuwa domin sana’ar sayar da goro.

Gabanin fitarsa, matarsa mai suna Asiyat Usman ta haifa masa ’ya’ya uku maza amma daga bisani duk sun rasu daya bayan daya, kamar yadda ya bayyana.

Matar ta ki ta bi shi zuwa Ibadan kuma bayan shekara hudu da fitar tasa, sai ya samu takardar saki daga gareta. Ya yanke shawarar ci gaba da tafiyar da rayuwarsa a hakan, ba tare da aure ko ’ya’ya ba.

Da yake bayanin dogon bulaguron nasa ga Dagacin Dakadtsalle da wadansu mutanen kauyen, Saidun ya ce shi tare da abokan kasuwancinsa sukan yi fataucin goro daga Ikenne zuwa Ibadan suna ciniki.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Shekara 73 bayan bacewarsa dattijo da aka yi tunanin ya dade rasuwa ya bayyana a kauyensa a Kano
Shekara 73 bayan bacewarsa dattijo da aka yi tunanin ya dade rasuwa ya bayyana a kauyensa a Kano Photo credit: The Cable
Asali: UGC

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

A cewarsa: “Mukan hadu da mahaifiyar Chif Obafemi Awolowo wacce ta dauke mu tamkar ’ya’yanta kuma takan kyautata mana sosai a kullum."

Daga bisani ya bar Ibadan inda ya koma Ado Ekiti bayan ya share shekaru 22 a can inda ya ci gaba da kasuwancin goro.

Shekara shida bayan nan ya sake koma wa garin Ipele, mai makwabtaka da garin Owo. A garin Ipele, ya yi adabo da sayar da goro inda ya koma sarrafa soso.

Sannan daga bisani ya ajiye ita ma sana’ar sarrafa soson inda ya koma na duke tsohon ciniki – wato noma.

Kakan mutumin da ya mayar da shi gida, Olumuyiwa, mai suna Joseph Adepitan ya kulla abokantaka da dattijo Saidu inda dattijon ya kasance yakan ziyarci gonar abokin nasa a koda yaushe.

A bangare guda, Gosiame Thamara Sithole mai shekaru talatin da bakwai ta haifi yara jarirai goma a daren Litinin, 7 ga Yuni; Mahaifiyar ta yi tsammanin za ta haifi yara takwas kamar yadda aka nuna a lokacin haihuwa amma an sake samun ƙarin jarirai biyu yayin haihuwar.

A cewar wani rahoto da Pretoria News da wasu kafafen yada labarai suka fitar, Thamara ta haifi yaranta maza bakwai da mata uku ta hanyar fida a cikin asibitin Pretoria.

Yanzu ta zama uwa mai yara 12 tunda dama tanada tagwaye ‘yan shekaru shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel