Wata mata ta haifi yara 10 a lokaci guda, ta karya tarihin duniya

Wata mata ta haifi yara 10 a lokaci guda, ta karya tarihin duniya

- Wata mata ‘yar kasar Afirka ta Kudu Gosiame Thamara Sithole ta samu karuwa da haihuwa jarirai har goma

- Thamara, mahaifiya ga‘yan tagwaye yan shekara shida, ta haihu a wata bakwai da kwana bakwai a asibitin Pretoria

- Mijinta cike da farin ciki ya ce jariran da aka haifa maza ne bakwai da mata uku ya kara da cewa haihuwar yaran ta sashi cikin murna da farin ciki

Gosiame Thamara Sithole mai shekaru talatin da bakwai ta haifi yara jarirai goma a daren Litinin, 7 ga Yuni; Mahaifiyar ta yi tsammanin za ta haifi yara takwas kamar yadda aka nuna a lokacin haihuwa amma an sake samun ƙarin jarirai biyu yayin haihuwar.

A cewar wani rahoto da Pretoria News da wasu kafafen yada labarai suka fitar, Thamara ta haifi yaranta maza bakwai da mata uku ta hanyar fida a cikin asibitin Pretoria.

Yanzu ta zama uwa mai yara 12 tunda dama tanada tagwaye ‘yan shekaru shida.

A cewar mijinta, Teboho Tsotetsi, cikin matar gaba kyauta ce daga Allah domin ba ta taba shan kowane irin maganin haihuwa ba.

A wata hira da aka yi da ita wata daya da ta gabata kafin ta haihu, mahaifiyar mai yara 12 a yanzu ta ce ta kadu matuka lokacin da aka sanar da ita cewa zata haifi yara da yawa.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Wata mata ta haifi yara 10 a lokaci guda,'ta karya tarihin duniya'
Wata mata ta haifi yara 10 a lokaci guda,'ta karya tarihin duniya' Hoto: Pretoria News
Asali: UGC

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

Wahalar ciki mara misaltuwa

Binciken da akayi a farkon shekara ya nuna tana ɗauke da yara takwas amma daga baya binciken ya nuna yara goma ne.

Sauran jariran biyu ba a iya gano su ba a lokacin kyankyasan su saboda sun bi bututu mai wuyar ganewa.

Ta tuna yadda ta kasance cikin shakku lokacin da aka sanar da ita cewa tana tsammanin yara da yawa sannan kuma ta ji tsoron yiwuwar ko zasu rayu.

Mijinta, wanda ba shi da aikin yi a yanzu ya ce ya yi matukar farinciki da zuwan jariransa duniya.

"Na ji kamar ina ɗaya daga cikin 'ya'yan Allah amma har yanzu na kasa gaskatawa. Nakosa inji narike su a hannuna," inji shi.

A wani labarin kuwa, Kwamandan Hisbah a jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hukumar Hisbah ta sasanta ma'aurata 3,079 a shekarar 2020 ya bayyana haka ne wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Dutse ranar Alhamis.

Mista Dahiru ya bayyana cewa sulhunta ma'aurata don tabbatar da zaman lafiya yana daya daga cikin hakkokin hukumar.

Ya ce hukumar ta kuma taimaka wajen sasanta rikice-rikicen da suka shafi ‘yan kasuwa 1,081, iyaye da yara, makwabta, da manoma da makiyaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel