Bidiyon 'yar Najeriya dake siyar da shinkafa dafaffa ta N10, tace tana samun riba

Bidiyon 'yar Najeriya dake siyar da shinkafa dafaffa ta N10, tace tana samun riba

- Wata mata 'yar Najeriya mai suna Margret Jimoh, wacce take siyar da abinci tun 1984 tace mugunta ce tasa ake kara kudin kayayyaki a kasar nan

- Da farashin abincinta a N10, matar ta bayyana cewa duk da arhar abincinta, riba tana shigo mata bayan ta yi cinikinta na kowacce rana

- Margret ta ce ta yanke hukuncin mayar da abincinta arha bagas ne bayan da take son saukakewa 'yan Najeriya

Wata mata 'yar Najeriya mai suna Margret Jimoh wacce aka fi sani da Shinkafar Maggi a Ado Ekiti, jihar Ekiti, ta nuna cewa 'yan kasuwa zasu iya samun riba koda basu daga farashin kayayyaki ba.

A wata tattaunawa da BBC News Yoruba tayi da ita, matar ta ce ta fara siyar da shinkafa tun 1984. Amma abun mamakin shine yadda take siyar da shinkafar naira goma-goma.

KU KARANTA: Twitter ta sha alwashin ba 'yan Najeriya damar amfani da ita duk da Buhari ya dakatar

Bidiyon 'yar Najeriya dake siyar da shinkafa dafaffa ta N10, tace tana samun riba
Bidiyon 'yar Najeriya dake siyar da shinkafa dafaffa ta N10, tace tana samun riba. Hoto daga BBC News Yoruba
Asali: Facebook

KU KARANTA: King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN

Matar ta bayyana cewa ta fara siyar da abinci a shekarun da suka gabata kuma da farko a kan naira biyar-biyar take siyarwa amma daga baya ta tada zuwa naira goma-goma.

Ta ce: "Dalilin da yasa na fara siyar da shinkafa a arha shine yadda abubuwa suke a kasar nan. Na fara siyar da shinkafa kan naira biyar-biyar..."

Ta ce jama'a da dama sun san ta a matsayin kawar matalauta saboda yadda take kasuwancinta ba tare da cin gagarumar riba ba.

Domin nuna cewa ba sadaka take ba, matar ta ce duk da farashin da take siyar da abincinta, tana samun riba kodayaushe.

Da kudi kamar naira hamsin, kwastoma zai iya siyan shinkafa isassa tare da nama a wurinta.

Margret ta bayyana cewa abinda take yi yana bude mata hanyoyin alheri, duk da tace akwai kalubale kamar lokacin da ruwan zafi ya taba zuba cikin idonta.

A wani labari na daban, manyan sojoji ashirin da tara aka tirsasa yin murabus daga aiki bayan nada Manjo Janar farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya.

Wannan tirsasa murabus din ya ci karo da ikirarin hedkwatar tsaro na makon da ya gabata wanda suka ce babu sojan da za a yi wa ritaya duk da nada Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa da Buhari yayi.

Yahaya mai mukamin Manjo Janar daga jihar Sokoto ya samu mukamin shugaban sojin kasa na Najeriya a ranar 27 ga watan Mayu bayan mutuwar Ibrahim Attahiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng