An damke hadimin gwamna Sule, yan sanda 2, Kansila da wasu 14 kan satan karafunan layin dogo

An damke hadimin gwamna Sule, yan sanda 2, Kansila da wasu 14 kan satan karafunan layin dogo

- Mai dokar bacci ya buge da gyangadi, mai hakkin kare dukiya ya sace

- Babban hadimin gwamnan Nasarawa ya shiga komar yan sanda

Hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke mai baiwa gwamna Abdullahi Sule shawara kan ayyukan alfanu da wasu mutum 16 kan laifin sace karafunan layin dogon jirgin kasa.

An damke wadannan mutane ne suna satan karafunan dake garin Lafiya da karamar hukumar Keana na jihar.

Kwamishinan yan sanda CP Bola Longe, ya bayyana hakan ranar Alhamis a Lafiya, inda ya bayyana mutanen.

Ya yi bayanin cewa mutanen da ake tuhuman sun kasance suna kasuwancin sayan karafunan layin dogo daga wajen barayi amma dubunsu ya cika yayinda yan sanda suka samu labari.

"Hukumar yan sanda ta cika hannu da malalata yayinda suke satan karafunan layin dogo a Agyaragu dake karamar hukumar Lafiya da kuma Anguwan Alago dake karamar hukumar Keana," yace.

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

An damke hadimin gwamna Sule, yan sanda 2, Kansila da wasu 14 kan satan karafunan layin dogo
An damke hadimin gwamna Sule, yan sanda 2, Kansila da wasu 14 kan satan karafunan layin dogo

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Yayinda Jaridar Punch taji ta bakin hadimin gwamnan, ya yi bayanin cewa bai san kayan sata ake sayar masa ba.

Yace: "Ni dan kasuwa ne. Ina da dillali mai kawo min kaya kuma na yadda da shi. Ya rasu yanzu.... Wannan shine karo na farko da suka kawo min karafunan layin dogo. Bayan da na saya, na sayar N3.6 million."

Daga cikin wadanda aka damke akwai jami'an yan sanda 2, jami'in NSCDC 1, tsohon Kansila 1 da kuma wani dan kasar Sin.

A bangare guda, yayinda aka kammala ginin layin dogon Legas zuwa Ibadan kuma ake shirin kaddamar da shi a Yuli, gwamnatin tarayya na shirin fara ginin Kaduna zuwa Kano, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ranar Juma'a.

A cewar Vanguard, Amaechi ya yi wannan jawabi ne yayinda ya kai ziyarar wajen gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Amaechi ya bayyana cewa jihar Kano na da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya saboda shahararta da harkar kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng