Dr. Isa Ali Pantami ya doke Takwarorinsa, ya lashe kyautar gwarzon Ministan 2020

Dr. Isa Ali Pantami ya doke Takwarorinsa, ya lashe kyautar gwarzon Ministan 2020

- Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya lashe kyautar Ministan shekarar 2020

- Jaridar Blueprint ta ba Ministan wannan kyauta saboda kokarin da ya yi

- Ma’aikatar sadarwa ta taimaka wajen ceto tattalin Najeriya daga kangi

An karrama Ministan tattalin arzikin zamani da sadarwa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin Ministan Ministoci na shekarar 2020 da ta gabata.

Jaridar Blueprint Newspaper ta shirya wannan biki a Transcorp Hilton a ranar 3 ga watan Yuni, 2021.

Rahoton ya ce Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya zo na farko wajen kashe wannan gasa, wanda shi ne na goma da jaridar ta shirya a shekarar da ta wuce.

KU KARANTA: FBI ta yi magana game da alakar Dr. Isa Pantami da Boko Haram

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi nasara ne saboda kokarin da ya yi a bangarori uku a wajen aikinsa – Tattalin arziki, yin keke-da-keke da kuma tsaro.

Jaridar ta ce Ministan tarayyar ya yi amfani da ofishinsa wajen bunkasa tattalin arzikin zamani, kawo gaskiya wajen aiki, da kuma inganta tsaron kasa.

Wadanda suka tsara wannan biki, sun ce bangaren ICT da Isa Ali Ibrahim Pantami yake jagoranta ta taka rawar gani wajen ceto tattalin arziki daga cikin kangi.

A cewar wadanda suka shirya wannan biki, kokarin da Ministan da hukumomin karkashin ma’aikatar suka yi, aka shawo kan tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA: Akwai yadda za a cigaba da more dandalin Twitter ba tare da an sani ba

Dr. Isa Ali Pantami ya doke Takwarorinsa, ya lashe kyautar gwarzon Ministan 2020
Dr. Isa Ali Pantami Hoto: www.techeconomy.ng
Asali: UGC

“Bangaren ICT ne wanda ya fi kowane zaburar da tattalin arzikin kasa a 2020, ya motsa da 14.7% a karshen 2020, hakan ya ceto kasar daga matsin tattali.”

Wadanda suka halarci wannan biki sun hada da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Mai girma Ministan ta bakin wani hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ya ji dadin samun wannan lambar yabo, ya ce zai kara zaburar da shi wajen kara kokari.

A shekarun baya kuna da labari cewa ‘Yan Jaridar Najeriya a karkashin Kungiyar nan ta NUJ ta ba Sheikh Dr. Isa Ibrahim Ali Pantami kyautar lambar yabo.

A wancan lokaci Isa Ibrahim Ali Pantami ya na rike da kujerar shugaban Hukumar NITDA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel